Kannywood

Tabbas Shugaban Hukumar Tace Fina Finau Ismail Afakallahu Ya Cika Namijin Duniya – Aliyu Imam

Wannan itace takardar gargadi wacce shugaban Hukumar tace fina-finai Malam Ismail Na’abba Afakallahu ya rattaba hannu wanda aka aikawa gidan TVn Arewa24 inda aka basu awa 48 kansu tsayar da shirin da suke haskawa mai suna “Kwana casa’in” da shirin “Gidan badamasi” idan har ba zasu bi dokokin da hukuma ta tanada ba, musamman yadda shirin ke cin karo da dokar haska fina-finai a jahar Kano, kamar yadda yaci karo da addinin musulunci da al’ada.

Malam Afakallahu ya gargadi gidan Arewa idan har basu ji wannan magana tasa ba, to ba zasu ki gani ba, domin abinda zai biyo baya bazai dadi ba.

Tun bayyanar sabon shirin Kwana Casa’in Zango na Uku mutane ke ta korafi, musamman ganin fuskar yarinyar data fitar da bidiyon tsiraici a baya, wanda a bayan ma hukumar tace fina-finan ta turawa gidan Tvn Arewa24 sako dasu cireta amma sukai kunnen uwar shegu, koda yake adalcin da zanyi wa wannan shiri shine, tun a lokacin nayi magana Tvn tace sunyi bakin ciki da fitar wannan Video matuka, amma matsalar shine an riga an dauki shirin da ita tuntuni, fitar da yarinyar daga shirin yana nufin sai dai a sake shirin baki daya.

Bayan wannan, a sabon shirin nasu Zango na uku mutane sun koka bisa ganin wasu abubuwa wanda basu saba gani ba, musamman taba jikin mata da Maza aka nuna suna yi wanda ya saba da addini da al’adar mutanen arewa.

Bayan fitowar wannan lamari na samu sakonni daga mutane da dama suna tambayata yaya akayi suka ga Safara’u duk da cewa naje na zauna da Shugaban wannan hukuma kuma ya bani labarin cewa ya aika da takarda a cireta? shin hakan yaudara ce daga wajensa? sannan gashi ma sun fara yin abubuwa wanda ba’a saba gani ba, shin wane aiki hukumar take da ta bari haka na faruwa?

Na baiwa mutane da dama amsa cewa suyi hakuri insha Allah Malam Afakallahu zai dauki mataki, wannan yasa jama’a kuka ga nayi shiru bance komai akan lamarin ba, domin tun a shekaranjiya nake tattauna lamarin da Malam Afakallahu wanda ko dazu da safe ya kirani a waya yana bayyana min matakan da zasu dauka. Alhamdulillah zuwa yanzu gashi an dauki wannan mataki, tabbas Afakallahu yayi matukar kokari, kuma yayi bajintar da ba’a taba tsammanin zai ba, domin gidan Arewa24 da kuke gani suna da daurin gindi daga turawan yamma.

A baya na shafe shekaru kusan hudu ina caccakar wannan bawan Allah, a tunanina baya tabuka wata tsiya a wannan hukuma, sai da ya gayyace ni muka zauna dashi ya bayyana min irin nasarorin daya samu, da irin fina-finan daya hana fitowa wanda sun kai guda biyar, da wasu matakai na doka da yake zartarwa wanda yasa da yawan ‘yan uwansa ‘yan film suke jin haushinsa kuma suke rigima dashi, ya nuna min takardu da dama na irin aikace-aikace da kokari da hukumarsa take da irin kalubale da suke fuskanta, a cikin fina-finan daya hana fitowa akwai wanda kungiyar CAN ta dauki nauyinsa domin tallata addinin kiristanci a arewa wanda har shari’a anyi dashi akan haka, abubuwan suna da yawa banson tsawaitawa.

Duba da wadannan dalilai, tabbas Afakallahu ya cancani ya samu adalci daga wajenmu, muna yaba masa, kuma muna addu’a Allah ya saka masa da Alkhairi ya dafa masa yaci gaba da taimakonsa cikin kokarinsa na tsaftace tarbiyar al’ummar arewa.

Indabawa Aliyu Imam

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button