Kannywood

Munyi Asarar Maƙudan Miliyoyin Kuɗi Saboda Cutar Korona Bairos – Kannywood

TUN bayan ɓullar cutar korona (‘coronavirus’ ko ‘COVID-19’) a Nijeriya harkokin kasuwanci su ka samu kan su a cikin wani mawuyacin hali wanda ba a taɓa ganin irin sa ba.

Hausawa sun ce abin da ya ci Doma ba ya barin Awai, don haka masana’antar finafinan Hausa (Kannywood) ma ta na ɗaya daga cikin sana’o’in da su ka faɗa cikin halin ha’ula’i.

Kannywood waje ne inda mutane sama da miliyan biyu su ke cin abinci. Annobar korona ba ta bar ‘yan fim ɗin ba, domin kuwa sun faɗa cikin mugun yanayi sakamakon tsayawa cak da harkokin kasuwancin su su ka yi.

A yau babu wani abu da ya ke gudana na kasuwanci a duk cikar masana’antar da batsewar ta. Wannan ya sa ‘yan fim sun yi asarar miliyoyin nairori, kuma su na cikin zaman haƙuri, musamnan ma da aka hana kowa fita.

Abubakar Bashir Maishadda, wanda babban furodusa ne, ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Magana ta gaskiya, yanayin da ake ciki a masana’antar mu tun bayan da aka hana zirga-zirga, musamman ma a Kano da Abuja, abin ya jefa mu cikin wani mawuyacin yanayi tare da yin asarar da ba za ta misaltu ba.

“Domin idan ka duba, a yanzu babu shutin ɗin fim, babu kasuwar da za ka je ka kai, ga gidajen talbijin sun daina karɓa, ga gidajen kallo duk an rufe.

“Don haka abu ne mai wahala ka iya faɗar yawan miliyoyin kuɗin da aka rasa, domin idan ka duba ko ɗan guntun fim da ake yi ana sakawa a YouTube yanzu ya tsaya saboda babu fita, gari a kulle.

“Haka su ma waƙoƙi, duk babu yadda za a je a ɗauka. Don haka a fili ya ke masana’antar mu ta yi asarar miliyoyin kuɗin da ba za su lissafu ba.”

Shi ma babban mashiryin fim, Alhaji Sani Sule Katsina, cewa ya yi, “To gaskiya masana’antar mu ta shiga wani hali, sai dai addu’a, domin idan ka duba da man kasuwancin fim ya mutu, don haka sai ‘yan dabaru.

“Kuma a da mu na kai finafinan gidajen talbijin, su ma su ka dakatar. Sai mu ka koma ɗorawa a ‘online’; ta nan ake samun kuɗi. To kuma da wannan koronar ta zo sai ta tsayar da komai.”

A hirar sa da mujallar Fim, Sani Sule ya ce: “Don haka a yanzu babu wani abu da ya ke gudana. Kowa a zaune ya ke.

“Don haka ka zo maganar cewar masana’antar ta yi asara ai abu ne da ya ke a fili, kowa ya na gani, domin asarar dubban miliyoyin da aka yi ba za su lissafu ba.”

Balarabe Murtala Baharu ya na ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a masana’antar finafinai ta Hausa. Shi ma ya bayyana wa mujallar Fim cewa: “Idan ka duba, masana’antar finafinai tun kafin wannan annobar da man ta na cikin wani yanayi, amma da annobar ta zo sai ta sake durƙusar da ita.

“Don haka idan mu ka kwatanta irin asarar da aka yi a zuwan wannan cutar, za mu iya cewa an yi asarar kuɗi aƙalla miliyan ɗari.

“Amma in da kamar lokacin da masana’antar ta na kan ganiyar ta ne, to asarar sai ta kai ta miliyan ɗari biyar.

“Don haka dai masana’antar ta yi babbar asara, musamman idan aka duba yadda komai ya tsaya a wannan lokacin.”

Shi kuma Hamza Dogo Ɗandago, shi ne mai kula da duk wani fim da za a nuna a gidan sinima na ‘FilmHouse’ da ke cikin harabar kantunan Shoprite a Kano. Mujallar Fim ta ji ta bakin sa dangane da halin da aka shiga. A nasa bayanin, ya bayyana mana cewar: “A yanzu komai ya tsaya, ba a haska fim a sinima, don haka babu wani kuɗi da ya ke shigowa masana’antar ta sinima.

“Ka ga kuwa ba ƙaramar asara masana’antar ta yi ba ta wannan ɓangaren, domin kuwa a sati idan aka haska fim, in dai babban fim ne, ana yin cinikin miliyan biyu zuwa uku; kai, wani ma har biyar ana yi. To ka ga yanzu ba a haska fim, saboda haka masana’antar ta yi babbar asara ta wannan ɓangaren.

“Don haka fatan mu a nan dai Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifa.”

A ɓangaren ‘yan wasa kuwa, mujallar Fim ta ji ta bakin fitaccen jarumi Abba Al-Mustapha, wanda ya bayyana halin da ake ciki da cewa: “Mu yanzu harkar mu a tsaye ta ke, don haka babu wani abu da ya ke gudana. An tsayar da komai.

“Domin harkar mu ta haɗuwar jama’a ce; duk wani abu da za a yi sai an tara jama’a, to sai ya zamo ita wannan cutar ta na hana taruwar jama’a waje ɗaya. To ka ga dole harka

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button