Addini
Audio : Cutar Korona Bairos Ba Annoba Bace, Bala’i Ne – Sheikh Abbas Jega
Shehin Malamin addinin Musulunci a Nigeria Ash-sheikh Abbas Jega, yayi bincike a duniyar ilmi ya duba manyan litattafai na addinin Musulunci ya gano cewa cutar Coronavirus ba annoba bace, masifa ne.
Ni Datti Assalafiy ban taba jin wani bayani da ya gamsar dani ba akan matsayar Coronavirus kamar jawabin da Malam Abba Jega yayi, na gamsu sosai dari bisa dari cewa Coronavirus ba annoba bace, masifa ne kawai Allah Ya aiko mana ta sanadin wasu domin ya jarrabi duniya sakamakon miyagun zunnubai da ake aikatawa
Manyan Malaman Musulunci na duniya sun tabbatar da cewa duk cutar da zata kama mutum bata kashe shi ba kasa da kwana uku to wannan cutar ba’a kiranta da cutar annoba, ba annoba bace, uwa uba Annabi Muhammad (SAW) yace har abada annoba ba zata sake shiga garin Makkah da Madinah ba.
Don haka inda Coronavirus annoba ce to da ba zata shiga garin Makkah da Madinah ba, bayan haka ta kanyi kwanaki sama da uku tana jikin mutum, kuma ana warkewa, ita kuma cutar annoba ba’a warkewa, idan ta kama mutum sai ta kashe, Malam Abbas Jega yace duk wanda Coronavirus ta kashe shi kar ku ce yayi shahada, ku nema masa gafara da afuwar Allah kawai
Malam ya karanta jawabi cikin wani Littafi da Anas bin Malik yake magana akan annoba, yace cutar da ake kira annoba itace cutar da zata kama mutum yanzu yanzu zuwa an jima kadan ta kashe shi, yace anyi annoba cikin garin Makkah na tsawon kwana uku, inda an kara kwana uku da cutar sai ta kashe kowa a garin Makkah , mutum 83 suka mutu cikin iyalin Anas bin Malik
Anas Bin Malik yace lokacin da annobar tayi tsanani a garin Makkah, sai da kowa ya kwashe kayansa da iyalansa aka koma bakin makabarta, ana jiran mutum ya mutu a bunneshi,
Akwai audio da Malam Abbas Jega yayi wannan jawabi akan cewa Coronavirus ba annoba bace, masifa ne Allah Ya jarrabi bayinSa da ita, kuma idan kowa ya tuba ya gyara tsakaninsa da Allah sauki zai samu, zan saka muku link domin saukar da Audio din.
Allah Ka sakawa Malam da alheri, Ka yaye mana wannan masifa Amin
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com