Labarai
Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da umurnin sakin Sanusi II
Advertisment
Babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a ta bayar da umurnin sakin tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga inda aka tsare shi a garin Awe na jihar Nasarawa bayan an cire daga kan mulki a ranar Litinin.
Mai shari’ar Anwuli Chikere ne ta bayar da umurnin sakamakon bukatar da shugaban lauyoyinsa, Latee Fagbemi (SAN) ya shigar a ranar Juma’a.
Kotun ta ce a mika takardan umurnin sakin Sanusi da dukkan hukumomin da suka tsare da shi.
Wadanda Sanusi ya yi karar su a kotun kan batun tsare shi suna hada da Sifeta Janar na ‘yan sanda, Muhammad Adamu; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi; Attony Janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da Ministan Shari’a na Najeriya, Mista Abubakar Malami (SAN).
Advertisment
Source: Legit.ng/hausa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com