Vanessa: Mawakiya ‘yar kasar Amurka ta Musulunta ta kuma Musuluntar da iyayenta
Wannan labarin wata mawakiya ce wacce Allah ya nuna mata hasken Musulunci kuma ta karbe shi, inda sanadiyyarta ya sanya iyayenta duka suma suka Musulunta
Vanessa wacce take ‘yar asalin kasar Amurka, a da tana bin addinin Kiristanci ne. Ta Musulunta a lokacin da take da shekaru 19 a duniya, kuma a lokacin ne take tashe a harkar waka. Legithausa na ruwaito.
Vanessa: Mawakiya ‘yar kasar Amurka ta Musulunta ta kuma Musuluntar da iyayenta
Tunda dama harkar waka take yi, zuwa wurin casu kullum ba komai bane a wajenta. Haka a lokacin ta hadu da tsohon saurayinta wanda yake shima Musulmi ne amma baya son wannan zuwa casu da take yi. Daga baya Vanessa ta yanke shawarar daina waka, inda hakan ya sa ta fara gane wacece, ita kuma ta fara samun kwanciyar hankali a cikin zuciyarta. Da farko da ta fara jin wannan yanayi a cikin zuciyarta tayi tunanin ko dan saboda soyayyar da take yiwa saurayin nata ne, amma a hankali ta fara gane cewa ta fara samun imani ne da kaunar addinin Musulunci a cikin zuciyarta.
Allah ya cika mata burinta a ranar masoya ta duniya (Valentine’s Day), sai saurayinta ya bata kyautar wani wa’azi na Nouman Ali Khan. “Wannan shine karo na farko dana ji wani ya fada mini gaskiya a rayuwata.” Cewar Vanessa. Tana matukar sha’awar saurayinta da addinin shi; yadda yake tsayawa yayi Sallah a kowanne lokaci idan aka kira Sallah.
Ta fara son Qur’ani da Musulunci bayan wani dan karamin lamari ya faru. Mahaifinshi ya gansu a cikin wani shago, to dama ya sanar da shi cewa yana koya mata addinin Musulunci. Bayan wannan duka iyayen shi suka fara koya mata addinin Musulunci. Suka zamo Malamanta na addini, kuma suka yi iya bakin kokarin su wajen bayyana mata komai a cikin addinin.
KU KARANTA: Da mijina na da rai da tuni Najeriya ta wuce yadda ake tunaninta a duniya – Cewar Turai ‘Yar Adua
Daga baya Vanessa ta karbi kalmar shahada. Tana jin dadin dokokin addinin Musulunci, kuma tana jin dadin yadda ta kara samun kusanci da Allah. Ta koyi yadda za tayi sallah da wasu surori na Qur’ani. Tun daga wannan lokacin ta ce baza ta kara cire hijabinta ba har abada.
Sai dai Vanessa ta samu matsala da iyayenta a lokacin da suka gano cewa ta Musulunta, inda suka yi fushi suka nemi su koreta daga gidansu baki daya, amma soyayyar da da mahaifi yasa suka kasa. Sai suka je suka samu faston su ya basu shawara cewa babu komai, domin kuwa addinin Musulunci shine mafi kusanci da addinin Kiristanci, saboda haka tunda tana so su kyaleta tayi abinta.
Haka suka hakura, amma hankalinsu bai gama kwanciya, kullum da dare sai sun dauko musu na addini tsakaninsu da ita, haka Vanessa tayi ta kokarin nuna musu ainahin menene addinin Musulunci.
A hankali suma suka yadda cewa addinin Musulunci shine addinin gaskiya, kuma suka Musulunta. Hakan ya sanya Vanessa cikin farin ciki matuka.