Kannywood

Na ja baya da harkar fim sakamakon wasu dalilai -Abbas Sadiq

Advertisment

Majiyar mu ta Northflix ta tattauna da daya daga cikin tsofaffin jaruman Kannywood, Abbas Sadiq, dangane da ci gaban da masana’antar ke samu.

Jarumin ya ce, “Gaskiya masana’antar Kannywood ta samu ci gaba sosai yadda ya kamata, kuma duk wannan ya biyo baya ne sakamakon hakuri, juriya tare da kaskantar da kai da manyan jaruman mu da kuma shugabannin wannan masana’antar da su ke yi. Misali shi ne jarumi, Ali Nuhu wanda kowa ya shaida cewa shi ne kan gaba a wannan harka, sannan babu wanda ya kai shi kaskantar da kai a cikin masana’antar Kannywood, kuma ba ya daukar kan sa wani ne duk da cewar ya na wannan matsayin, kuma har yanzu ya na kan samun ci gaba a cikin masana’antar. Bayan nan kuma akwai sauran su irin su, Yakubu Muhammad, Sani Danja, Adam A Zango, Falalu Dorayi da sauran su, duk sun taka rawar gani a masana’antar wajen samar da ci gaban ta, kuma sun zauna lafiya da kowa, domin babu wani ko wata da za a nuna a matsayin abokin fada ko abokin rigima, ina ganin wannan nasara ce sosai a masana’antar ta mu, domin samun nagartattun mutane, shi ne ci gaban ko wacce masana’antar.Inji Abbas.

“Kuma Alhamdulillahi, sana’ar fim ta kawo mun ci gaba da dama a wasu abubuwa da na ke yi, amma na ja baya da sana’ar fim ne, saboda ba na son na takura kaina, saboda ina da wasu abubuwan da dama da na ke yi, ba wai iya fim ba ne kawai sana’a ta”. A cewar Abbas Sadik.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button