Me Yayi Zafi ! Zamu Dakatar Masana’antar kannywood – Abdul Amart Mai Kwashewa
Fitatce mai shirya fina-finai a cikin masana’antar Kannywood, Abdul Amart Mai Kwashewa, guda daga cikin muhimman mutane kuma fitatcen furodusa a masana’antar, ya bayyana cewa akwai yiwuwar su dakatar da masana’antar Kannywood zuwa nan da wani lokaci kadan har sai sun gyara irin tarin matsalolin da masana’antar ke fuskanta a halin yanzu.northflix na ruwaito.
Da majiyar mu ke tambayar sa shin ko menene shirin su na yin hakan?
Sai ya amsa mana da cewa ” Gaskiya mun yi shirin da ba a taba yin irin sa ba a masana’antar Kannywood, saboda tashin farko mun samar da zaman lafiya da hadin kai na shugabanci a tsakanin kungiyar Arewa Film Maker’s Associations da kuma MOPPAN. Wanda mu ka yi zaman fahimtar juna ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairu na shekarar nan da mu ke ciki, kuma zaman ya yi armashi mun kuma ta shi cikin farin ciki da fara’a yayin taron, wasu daga cikin cigaban da muke shirin kawo su cikin masana’antar su ne kamar haka, mun zama tsintsiya daya ma daurin ki daya, kuma dole kowa sai ya bi doka tare da yin mubaya’a ga shugabancin masana’antar, sannan yin hakan shi ne mataki na farko da zai kawo ma na hadin kai kafin muce zamu fara sauran abubuwan da muka sa a gaba. Kuma zamu bude ofisoshi a dukkanin jihohin Arewa wanda shi ne zai bada damar ko wane jarumi ko jaruma su tafi jihohin su domin su yi rijista a kuma daura sunayen kowa a kan shafin internet domin zama cikakkun yan fim, hakan shi ne zai bada damar mu san mu nawa ne a cikin masana’antar tun da kowa zai zama muna da cikakken bayanin sa da inda ya fito da kuma wanda ya tsaya masa kafin shigar sa cikin masana’anatar”. Inji Mai Kwashewa.
Ya kuma ci gaba da cewa” Yin hakan shi ne zai sa mu samu ci gaba da fadada kungiyar ta kai wani abu a duniya, tun da abun ya zama kamar a kungiyance ne, duk inda zamu shiga dole ne a karbe mu hannu bibiyu, kuma a bamu martaba tun da mun san yawan mu sannan kuma sunan kowa ya na kan shafin internet. Kuma dokar za ta fara aiki nan bada jimawa ba wanda babu gwamnati a ciki, saboda dokar mu ba zamu karya dokar gwamnati ba, toh itama kar ta shigo ta karya muna dokar mu, duk wanda ya yi ba daidai ba, dole ne ko waye shi, sai doka ta hukunta shi tare da dakatar da shi a masana’antar. Baya ga haka kuma zamu bada karfin gwiwa wajen tallata fina-finai a kafafen sadarwa da kuma manhajoji domin samun gyaran kasuwanci fina-finai”. Inji Abdul Amart Mai Kwashewa.