Labarai

Ku daina mana ta’aziyya, ba mutuwa aka mana ba – diyar Sunusi II Yusrah

Biyo bayan tsige tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II mai murabus, diyarsa ta fito a kafar sadarwar zamani ta Twitter tana yin gargadi tare da kashedi ga masu jajanta musu, inji rahoton TheCables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito diyar Malam Sunusi mai murabus, Yusrah Sunusi ta yi kira ga abokan huldarta a kafar sadarwar zamani ta Twitter da cewa su daina jajanta musu saboda ba mutuwa aka musu ba, kuma basu mutu ba.

A ranar Litinin, 9 ga watan Maris ne sakataren gwamnatin jahar Kano, Usman Alhaj ya sanar da amincewar gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ga tsige Malam Muhammadu Sunusi a matsayin sarkin Kano.

Kuma zuwa yanzu Gwamna Ganduje ya nada tsohon Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin masarautar Kano, bayan manyan fadawan masarautar masu nada Sarki sun mika sunan Aminun.

Sai dai diyar Sarki mai murabus ta bayyana ma abokanta a Twitter cewa: “Ku daina turo min da ‘Innallillahi wa Inna ilayhir raji’un’ da wai ‘Muna muku jaje’ saboda ba mutuwa muka yi ba.

“Ta yaya ya zamo ma ni ne nake tausan abokaina, ina fada musu “Ku yi hakuri” “Allah ne Ya so” “Inshaa Allah hakan yaafi alheri, ku saurare ne domin kuwa zan cajeku kudin tausan da nake muku.” Inji ta.

Sanin kowa ne dai Musulmai na ambaton ‘Innallillahi wa Inna ilayhir raji’un’ ne a duk lokacin da wani musifa ta fada musu, wanda yake nufin “Daga Allah mu ke, kuma zuwa gare shi zamu koma.”

Jim kadan kafin a sanar da labarin tsige mahafinta, Yusrah ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: “Za ku iya dakatar da shi, amma ba za ku iya dakatar da gaskiya ba, mutumin da ya raine ni bai taba tsoron rasa kujerar sarauta saboda mutuncinsa ba.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button