Kannywood

Idan gwamnati ta ba mu dama za mu fadakar a kan cutar Corona -Mai Shadda

Advertisment

A wata hira da mu ka yi ta musamman da daya daga cikin manyan masu shirya fim a masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Mai Shadda, ya bayyana wa majiyar mu cewa sun shirya tsaf domin yin fim din da zai wayar da kan jama’a dangane  da sabuwar cutar nan da ta bulla mai suna Corona Virus.

Furodusan ya bayyana hakan ne a lokacin da su ke ganawa da wakilin mu, a kan shirye-shiryen da su ke yi domin yin wani kwarya-kwaryan fim da zai wayar da kan jama’a a kan cutar ta Corona Virus .

Furodusan ya fara da cewa “Shirin wayar da kai na cutar Corona Virus, hakki ne da ya rataya a kan gwamnati, ba a kan mu ‘yan Kannywood ba, amma idan gwamnati ta bukaci mu yi wani shirin wasan kwaikwayo domin wayar da kai ai za mu yi, tun da ita za ta dauki nauyi ta kuma hada mu da likitoci kwararru ma su bincike a kan cutar su nuna ma na hanyoyin da za a bi domin magance ta, amma hakan nan ba za mu dauki jiki mu fara shirin wayar da kai a kan cutar da mu kan mu bamu san yadda zamu magance  ta ba, ballan ta na mu wayar wa da jama’a kai”. A cewar Mai Shadda.

Ya ci gaba da cewa, “Amma za mu yi matukar murna, har idan gwamnati ta jawo mu a jiki ta kuma bamu karfin gwiwar yin wannan shirin da zai iya zagayawa duk duniya ba wai iya Nijeriya kadai ba”. Inji Mai Shadda.

Advertisment

Daga karshe, ya yi kira ga jama’a a kan a yi ta addu’a domin Allah ya kawo karshen wannan cutar ta Corona Virus ya kuma kare mu baki daya.northflix na wallafa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button