Kannywood

Duk Wanda Ya Fitar Da Bidiyon Tsaraici Na, Sai Allah Ya Saka Min, Cewar Safara’u Kwana Casa’in

Advertisment

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Jarumar finafina Hausa wadda ta fito cikin shirin Kwana Casa’in, wacce aka fi sani da Safarau ta yi Allah wadai ga masu zaginta a kafafen sada zumunta saboda wani bidiyon ta da ya fita aka nuno ta tsirara.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani gajeren bidiyo inda aka nuno jarumar na sharbar kuka tana cewa duk wanda ya tona asirin wani shi ma nasa ba zai rufu ba.

Jarumar ta ce “abin haushi mutane sai su rinka zagin ‘ya’yan mutane a soshiyal midiya? Tace ku yi ta yadawa. Duk wanda ya yi min shi ma idan Allah ya yarda kafin ya mutu sai an yi wa ‘yar uwarsa”.

Ta kuma kara da cewa insha Allah duk wanda ya fitar da wannan bidiyon sai Allah ya saka mata.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button