An Zargi Mawaki Hamisu Breaker Da Yaudaro Matar Aure Zuwa Cikin Harkar Fim
Ana zargin shahararren matashin mawakin finafinan Hausa, Hamisu Breaker Dorayi da laifin hurewa wata matar aure kunne har sai da ya yaudaro ta zuwa cikin harkar fim din Hausa.
Ba kowa bace ake zargin Breaker ya hurewa kunnen illa yarinyar da ake yawan ganin yana daukar wakokin bidiyon sa da ita, wato Momee Gombe.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Momee Gombe ta taba auren daya daga cikin mawakan Hausa, wato Adam Fasaha wanda kuma na hannun daman Hamisu Breaker din ne.
A yayin jin ta bakin na hannun daman Adam Fasaha, wato Aliliyo Mai Waka, ya bayyana cewa shekaru biyu da suka gabata, Adam Fasaha ya auri Momee Gombe, amma sai Hamisu Breaker ya dinga hure mata kunne ba tare da ya yi laka’ari da cewa tana gidan miji ba, inda har ta kai ga asirin sa ya tonu har ya nemi gafarar abokin nasa kan cin amanarsa da ya yi. “Ina zargin Hamisu Breaker da hannu dumu-dumu a mutuwar auren abokina kuma aminina wato Adam Fasaha”, cewar Aliliyo Mai Waka.
Aliliyo ya kara da cewa a yanzu irin wannan cin amanar ya zama ruwan dare a masana’antar fim din Hausa. Domin irin hakan ya faru tsakanin Adam A. Zango da tsohuwar matarsa Maryma A.B Yola, inda bayan ta fito daga gidan sa wasu ‘yan fim suka dinga yi mata wasu abubuwa domin a ci mutuncinsa. Haka kuma an yi wa mawaki Adamu Hassan Nagudu, yanzu kuma an dawo kan Adam Fasaha.
Aliliyo ya kara da cewa abin haushi da takaici shine yadda bayan kwana biyu da saki dayan da Adam Fasaha ya yi wa Momee Gombe wasu daga cikin ‘yan fim suka tafi da ita jihar Bauchi yin aikin fim inda suka dauki tsawon mako guda a can. Inda ko idda ba a bari ta yi ba. Kuma a daidai lokacin Adamun yana kokarin ganin ya mayar da ita gidansa tunda dama saki daya yi mata.
Wadanda ake zargi da daukar jarumar zuwa Bauchi yin fim a wannan lokacin sune Nura Mustapha Waye, Boothcut, Mai Gaskiya da sauransu. Inda aka kama Boothcut da Waye bisa wannan laifin.
Aliliyo bai tsaya a nan ba ya kara da cewa ko shi Hamisu Breakan an so a kamo shi a lokacin, amma Adam Fasaha ya ce a bar shi saboda alakar dake tsakanin su.