Mawaki Nazifi Asnanic Ya Shiga Sahun fitattun mutanen 10 A Jahar Kano
Wani bincike da aka gudanar ya zakulo shahararren mawakin nan na Kannywood da bukukuwa, Mallam Nazifi Asnanic daga cikin fitattun mutane 10 a jahar Kano.
A bisa ga binciken wanda jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram na @nazifiasnanic ya nuna cewa mawakin ne na tara cikin sahun fitattun mutanen 10 a jahar Kano.
An tattaro cewa Nazifi ya shiga sahun wadannan mutane saboda gudumuwarsa a harkar nishadantarwa da taka rawa a fina-finan hausa.
Sauran fitattun mutanen da binciken ya zakulo su ne: Marigayi Sheikh Aldulsamad Isyaku Rabiu, Engr. Mohammad Rabiu Musa Kwankwaso, AlhajiAliko Dangote, Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayer, Marigayi Aminu Kano, Alhaji Aminu Dantata, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, Farfesa Mohammed Bello da kuma Amina Namadi Sambo.
Ga yadda mawakin ya wallafa a shafin nasa: “Fitaccen mawakin @nazifiasnanic yana matsayin na Tara cikin shahararrun mutanen 10 da binciken ya zakulo.
“Sauran fitattun mutanen su ne: Marigayi Sheikh Aldulsamad Isyaku Rabiu, Engr. Mohammad Rabiu Musa Kwankwaso, Alh. Aliko Dangote, Marigayi Sarkin Kano Alh. Ado Bayer, Marigayi Aminu Kano, Alh. Aminu Dantata, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, Prof. Mohammed Bello da kuma Amina Namadi Sambo.
“Nazifi ya shiga sahun wadannan mutane saboda gudumuwarsa a harkar nishadantarwa da taka rawa a fina-finan hausa.”
A wani labarin kuma, mun ji cewa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bawa mabarata da masu neman taimako shawarar cewar su daina rokon jama’a da ‘yan uwansu, su mika kokon bararsu ga gwamnati.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Sanusi II ya fadi hakan ne a wurin taron Alarammomi da cibiyar karatun Qur’ani a Najeriya ta shirya mai taken; “tsaftace Almajiranchi domin fuskantar rayuwa ta gaskiya.”
Basaraken ya bukaci iyaye su daina tura yaransu makarantun Almajirci, tare da bayyana cewa yara zasu iya koyon karatun Qur’ani a makaruntun unguwanni da garuruwansu.