Kannywood

Karanta Yadda Jaruman Kannywood Su Ka Taya Maryam Booth Alhini

DAGA IRO MAMMAN, Mujallar Fim

DIMBIN fitattun jaruman masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood sun taya Maryam Booth baƙin cikin abin da ya faru gare ta na ɓullar wani guntun bidiyo inda aka gan ta tsirara.

Ɓullar bidiyon a ranar Talata ya haifar da ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya inda mutane su ka dinga furta albarkacin bakin su.

Jarumai irin su Ali Nuhu, Sani Danja, Ado Gwanja, Rahama Sadau, Mansurah Isah, Amal Umar, Tumba Gwaska da sauran su da dama sun fito sun yi maganganun yi wa jarumar kara a daidai wannan lokaci da ta ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

Jaruman sun nuna mata cewa wannan abu da ya faru muƙaddari ne, don haka kada ta damu, sa’annan da yawa sun roƙi Allah da ya yi mata sakayya.

Wata alama ta goyon baya da kyakkyawar jarumar ta samu ita ce buɗe wani shafi na musamman da wani ya yi a Instagram mai taken ‘I Stand With Maryam Booth” inda ya ke kamfen ɗin kare martabar jarumar ta hanyar tattaro bayanan da ke nuna ƙauna a gare ta daga shafukan wasu ‘yan fim ɗin.

Idan kun tuna, mujallar Fim ce ta fara bayyana cewa jami’an tsaro su na farautar wasu mutane biyu, mace da namiji, waɗanda ake zargin su ne ummulhaba’isin ɓullar bidiyon.

Duk da yake mujallar ba ta ambaci sunayen matasan biyu da aka faɗa mata ba, washegari an fallasa sunan ɗaya daga cikin su, wato mawaƙin hip-hop Ibrahim Deezell.

Amma mawaƙin ya fito ya ƙaryata zargin da ake masa, ya ce ba shi ba ne ya fitar da bidiyon.

Sai dai kuma a jiya Maryam Booth ta fito ta ce ba shakka Deezell ne ya ɗauki hoton bidiyon. Amma kuma ba ta ce shi ne ya yaɗa shi ba.

A nan ƙasa, ga wasu daga cikin ra’ayoyin goyon bayan da Maryam Booth fitattun ‘yan fim su ka yi mata mujallar Fim ta tattara.

Mujallar ta fassara wasu ra’ayoyin daga harshen Turanci, yayin da ta bar na Hausa a yadda su ke in ban da editin na nahawu:

AMAL UMAR: “‘Yar’uwa, mu na ƙaunar ki ƙwarai da gaske kuma mu na tare da ke a ko wane irin yanayi.

“Babu abin da ke ɗorewa, kuma duk wannan abu zai zo ya wuce in-sha Allahu.

“Babu wanda ya isa ya wuce wa ƙaddarar rayuwar sa. Mu na ƙaunar ki sosai kuma babu abin da zai sauya hakan.”

SANI DANJA: “Ci gaba jimiri ‘yar’uwa ta. Allah kaɗai ne zai iya karya ɗan’adam, ba wani mutum ba.”

MARYAM KK: “Wallahi a kan Maryam sai inda ƙarfi na ya ƙare. Ba ni magana a soshiyal midiya, idan aka ƙure ni zan yi. Kowa da ƙaddarar sa kuma babu wanda ya fi ƙarfin ƙaddara.

“Kowa ya san Maryam ba ta cikin wa’yannan masu nuna tsiraici. Kuma ni Maryam KK ina tare da ke Maryam Booth.”

ADO GWANJA: “Ciwon ki namu ne Maryam. Ba wanda ya fi ƙarfin ƙaddara ta hau shi a duniya, in kuma akwai ya faɗa mu ji. Aljanna ta Allah ce, kuma ke Musulma ce, Maryam.

“Kuma mu mu na tare da ke har abada. Kuma wallahi ba ki tozarta ba, don sharri dodon ɗan aike ne kuma zai koma wa mai shi, in-sha Allahu Rabbi.”

ALI NUHU: “Ya Allah, babu abu mai sauƙi sai wanda ka sauƙaƙa. Ina addu’ar ka sauƙaƙa mata a daidai wannan mawuyacin yanayi. Ki ci gaba da ƙarfin hali ‘ya ta, kuma ina addu’ar Allah ya yi mana tsari daga duk wani ƙulli na maƙiyan mu.”

NAFISAT ABDULLAHI: “Ubangiji Allah ya bi miki haƙƙin ki, ya tona asirin duk wayanda da sa hannun su. Mu kuma duk mai nufin mu da makamancin hakan, Allah ya nisanta mu da su. Ameen ya Allah.”

FALALU ƊORAYI: “Ba na goyon bayan duk wata ɓarna, yin ta ko yaɗa ta… Na fi yadda da umarnin idan ka ga ɗan’uwan ka cikin ɗabi’a mara kyau ka zamo mai masa nasiha da jan hankali ba ka tozarta shi ba.

“Ya fi zama alkairi ga mumini ya rufe asirin ɗan’uwan sa a kan tona asirin sa. Domin dukkan mu masu laifi ne, Allah ne ya ke rufa namu asirin.

“Allah ya kiyaye mu daga dukkan masifa da sharrin kan mu da na Shaiɗan.

“Ya na da kyau mu san abokin mu’amala, ba kowa ne ke zaune da kai saboda Allah ba.

“Mai aiken sharri domin tozarta wani YA BAR ƘOFAR SA A BUƊE.”

RAHAMA SADAU: “Duk wanda ya tozarta wani, Allah zai tozarta shi. Allah ya isa abin da aka yi wa Maryam Booth. Haba!!!”

MANSURAH ISAH: “Abar ƙauna ta da so na, ina alfahari da ke a ko yaushe. Ina matuƙar ƙaunar ki. Ba ki taɓa ba mu kunya ba, kuma za mu ci gaba da yin alfahari da ke.

“Ki na da ƙarfin hali, kuma zan ci gaba da son ki a dalilin hakan. Babu abin da zai girgiza ki, kuma babu abin da zai sauya mana tunani a kan ki.

“Rayuwa ba ta da tabbas, kuma idan abu ya riga ya faru sai kawai mu ci gaba da gudanar da rayuwar mu. Inji

“Yarabawa su na cewa: Arí írú éléyí rí, anfi dáru bá ólóró ni (sai ka nemi mai fassara). To ina ƙaunar ki kuma ba zan taɓa janye so na daga gare ki ba ‘yar yarinya ta.

“Ci gaba da jimiri. Allah ya san abin da ya sa haka ta faru gare ki.

“Kuma wannan ‘yar iskar ƙawar taki Allah ya gafarce ta domin kuwa za ta sha mamakin rayuwa. Sai ta yi aure miji na mutuwa ko ta yi hatsari ko wata ciwo mara magani ya kama ta. Lokacin za ta san abin da ta yi a baya.”

TEEMA MAKAMASHI: “Ɗaukaka ce za ta biyo baya, my darling. Kar ki damu, mu na tare da ke. Allah ya saka miki.”

TUMBA ABUBAKAR (GWASKA): “Allah Sarki ‘yar’uwa ta! Ni dai ba zan taɓa mantawa da halaccin da ki ka mini ba. Ku ne ku ka fara sa ni a fim, na tashi a gidan ku. Don haka ƙaddara ce, ta na kan kowa.

“Maryam ki yi haƙuri, wannan jarabawa ce. Ubangijin Allah ya sa ki ci wannan jarabawar, ya sa haka shi ne alkairi a rayuwar ki.

“Mu na tare da ke ko wuya ko daɗi. Maryam ba zan taɓa gudun ki ba kuma ba zan taɓa zama na zage ki ba saboda ke ‘yar halak ce.

“Ina miki son da Amude ya ke miki. Maryam ke sheda ce sai dai ki faɗa wa wani.

“Maryam duk wanda ya miki wannan tozarta Allah ya gaggauta saka miki, ya tona mishi asiri duniya da lahira. I luv u so much my dear luv.”

AMAL UMAR (Amsar da ta ba wani): “E, mun goyi bayan ta ɗin. Ka na so mu guje ta don kawai an mata bidiyo tsirara? Ba ku gan ta da wani ba, ba ku ga ta na wani abu ba. Mu yanzu ba mu damu da abin da wani zai ce ba.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button