Uncategorized

Illar Bayyana Sirri A Tsakanin Ma’aurata

 – Wani masani na cewa, “aure ya fi dadewa idan ya zama ma’auratan na boye sirrukansu a tsakanin su.”

Hakika, wannan haka yake. Sirrin ma’aurata wani abu ne da ya kamata ma’auratan su bar wa kansu a tsakanin su, ba tare da wani na ukun su ya ji ba komin ganin yanda su ke ganin kusancin shi a wurin su.

A kowace irin zamantakewa, akwai samun sabani da rashin jituwa da kan bijiro a wani lokaci. Zamantakewar aure zama ne da yake bukatar hakuri da juna, da kuma boye sirruykan rashin jituwa ba tare da bayyanar da ita ga wani na ukun ma’auratan ba. Akwai abubuwa da dama da ke taimaka wa dorewar aure, daga ciki, akwai boye sirrukan ma’auratan.

Ba wai yin auren ba, a’a ya za a yi a samu karko a zaman auren, wannan shi ne abunda yafi muhimmanci musasmman in an yi la’akari da yawaitar macecen aure a wannan lokacin. za ka samu wasu ma’auratan, da zaran matsala ta shiga a tsakanin su, sai kaga cikin sauri sun fada wa abokai ko kuma ‘yan uwansu, wanda kuma hakan yana da matsala.

Wani abu shi ne, zai iya kasancewa, wasu daga cikin wadanda mutum ke tunanin fada wa matsalar da ke tsakanin su, daman abund su ke jiran faruwarsa kenan, waton matsala a zaman na su.
Abunda ke biye, illolin bayyana sirrukan zamantakewa ne, wanda ma’auarata ya kamata su guji aikatawa domin kaucewa samun matsala.

Bata Suna:

Dayawan ma’aurata basa son duk lokacin da su ka samu matsala a tsakanin su dayan ya dauke ta waje zuwa ga abokai ko ‘yan uwa, hakan zai iya jawo suka da zagi wani lokacin.

Wata illar kuma, koda bayan kun shirya a tsakanin ku matsalar ta wuce, to shi wanda ku ka kai wa karar zai ci gaba da kallon wannan a tsakanin ku, wanda kuma hakan zai iya haifar da wata matsalar. Alal mislai, ta yiyu mijinki ko matarka na aikata wani abu da bai kamata ko kuma ba ka/ki so, to bayan ka/kin fadawa wani sai kuma ku ka daidaita a tsakanin ku, mai aikata wannan halin ya bari, to shi wanda a ka fadawar, ba lalle ya daina kallon wannan da abun ba, saboda haka, gara tun farko a yi hakuri idan dai ba abuin ya wuce wuri ba ne sosai ta yanda dolen sai an fada.
Ba Lalle Da Ma Kowa Na Farin Ciki Da Auren Ku Ba:

Akwai wadansu mutanen da su sun samu matsala da abokan zamansu (miji ko mata), ko kuwa daman ba su yi auren ba kuma su na jin haushin cewa ni ban yi aure ba amman wance ta yi aure (wannan kamar za a iya cewa ya fi faruwa ga mata), saboda haka su basuki kun samu matsala ba, kuma lalle, hakan na faruwa. Nan kuwa, a zaton mutum, masoyinsa ne da har zai iya daukara matsalar abokin zaman sa ya fada ma sa.

saboda haka, ya kamata mu guji fadawa mutane matsalar da ke tsakaninmu a matsayin ma’aurata, domin ba lalle ne wanda mu ke tsammanin masoyinmu ba ne ya zama hakan da gaske, wani/wata daman irin raanr da su ke jira su ji ta faru kenan. Sannan kuma ma dai, idan ku ka bar sirrinku atsakanin ku, ba wani wanda ya isa ya yi maku kustse ko katsalandan bare ya haifar maku da matsala.

Saka Yawan Damuwa:

Wannan kalar nau’in damuwar ta fi faruwa a wannan zamanin na soshiyal midiya. Za ka samu, wasu mutanen, duk abunda ya ke faruwa da su sai su yi wuf su je kan soshiyal midiya su tallata, wannan kuwa ko da matsalar zamantakewar auren su ne, wanda sam bai kamata ya zama hakan ba. Yin hakan kuwa, yana haifar da illa da damuwa sosai ga aboki/ abokiyar zama.

Zaman aure zama ne mai wahala da yake bukatar hakuri, yafiya, kau da kai, kai zuciya nesa tare da tausayawar juna, bama dai kamar tausayawar juna din. tausayawar nan kuma ta kunshi abubuwa da dama, har da tausayin ya mijina/matata za ta/ya ji idan na yi wannan? Baikamata ba tallata matsalar da ke tsakaninku ga wasu da su daman ba sun tamabaye ka/ki ba ne. To ina dalilin tallata kan ku a duniya (soshiyal midiya)?

Abunda ya kamata shin ne, matsalar ma’aurata ta kare a tsakaninsu, ba wai sai sun kai ta waje ba da hakan zai jefa akokin zama a cikin damuwa na jin cewa an tallata shi.

Janyo Tsana Ga Abokin Zama:

Kusan duk lokacin da mutum zai kai karar abokin zaman sa ga wani, to a irin son rai na dan adam,ya kan fadi laifin dayan ne kawai ba tare da fadar nasa ba, wanda yin hakan, kan iya yin tasiri a wurin wanda a ke fadawa din, wanda kuma zai iya janyo zai iya dora laifi da karan tsana ga wanda ake kai karar.

Wato abunda ya kamata dai, duk lokacin da ma’aurata su ka samu wani sabani, to su yi kokarin daidaita wa a tsaknin su, bayyaan matsalarsu ga wasu ba lallai ya zama mafita ga matsalar ba, wanda idan ya zama haka, an yi biyu da biyu kenan, sun fallasa kan su a lokaci daya kuma ba a cimma bukata ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button