Har idan wani zai tona asirin wani tabbas Kannywood za ta watse – Alhassan Kwalle
Jarumi Alhassan Kwalle, ya bayyanawa majiyar mu cewar idan har Kannywood za ta ci gaba da tafiya yadda take A yanzu wani na sukar wani, wani na bakin ciki da samun wani sannan wani ya na son tonawa wani asiri, to za a iya wayi gari watarana babu masana’antar gabadaya, ko kuma idan akwai to masu mutuncin basu da yawa.northflix na Wallafa.
Jarumin ya fadi haka ne a sakamakon wata tattaunawa da majiyar mu ta yi dashi kamar haka:
Matsayin ka na babba, Uba kuma shugaba a masana’antar Kannywood, me za ka iya cewa dangane da gutsiri tsoman da ba ya karewa a masana’antar?
“To yawanci idan kin ga irin wannan abu ya na faruwa a cikin al’umma to dalili biyu ne zuwa uku, ko dai mutane sun cika da jin dadi har sun rasa yadda za su yi da dadin da Allah ya yi musu, sai su koma su na kushe kan su kamar yadda mutanen mu su ke a yanzu, Ko kuma idan rashin abun yi ya yi yawa to shi ma ya na kawo irin wannan abun. Sai kuma abu na karshe jahilci duk inda jahilci ya yiwa mutane yawa a waje to komai ma zai iya faruwa”.
To ya ya ka ke ganin tafiyar Kannywood idan har wannan abun zai ci gaba da kasancewa?
“Indai har hakan zai ci gaba da kasancewa to ina da tabbacin za a wayi gari babu Kannywood, idan ma akwai to masu mutuncin ‘yan tsirari ne, domin duk wanda zai zubar da mutuncin wani to hadda na sa mutuncin ya zubar, kuma idan har ba za ka bi wanda yake sama da kai ba, babu yadda za a yi na kasa da kai ya bika”.
Akwai wani abu da ku ke yi wanda za su magance wannan matsalar a matsayinka na babba a masana’antar?
“Kin san yanzu ko da ni na tsuguna na haife su, sai kin ga ya zamana ka haifi da, ba ka haifi halinsa ba, kuma mu da muka dade kuma muka bada gudunmawa wajen kafa wannan masana’anta mun dauki wannan abu a matsayin jarabawa ne kawai, domin haka muna ganin wadannan da suke jawo fitintinu a matsayin wadanda Allah ya jarabce mu da su, tun da ko ba komai ba haka muka taso muka ga manyan mu sun yi ba kuma mu ma ba mu yi haka ba. Amma abun mamaki sai ga su yara sun zo daga baya, kuma Allah ya taimake su sun tarar an kafa, amma sun zo su na nema su ruguza wannan hakan sam ba daidai bane, domin haka muna kallon wannan a matsayin jarabta, kuma Alhamdulillahi yanzu mun dukufa yin azumi mun kaiwa Allah kukan mu muna fatan kuma ya dafa mana. Kuma muna nan muna addu’a duk mutumin da yake haddasa ma na fitina ko da ni ne Allah ya yi mana maganin sa, domin ba mu kafa wannan masana’antar domin a rinka cin zarafi ba ko a lalata al’umma mun kafa ta ne domin mu rufawa kan mu asiri mu karu wasu ma su karu”.
Me ka ke ganin ko ince mene ra’ayin ka dangane da yadda wasun ku su ke cewa rashin shugabanci shi ne babbar matsalar Kannywood din?
“Su wadanda su ke cewa rashin shugabanci wa suke bi a Kannywood? Idan ka na shugaba ka kira taro ba kowa zai zo ba, idan ka ga a na yi maka biyayya ko ka fada wani ya bika to farkon zuwa ne ya na so ya samu kafuwa, da mutum ya kafu ya samu yadda ya ke so sai ya mayar da kai ba ka san abun da ka ke ba, sai ya zo ya fi karfinka. To abun da ya sa bama damuwa da wannan, zan iya kiran sa da wani hali namu na Hausawa, duk inda bahaushe ya ke ka ce masa ya zo za a kafa kungiya to za a watse kowa ya kama wata hanya daban, domin haka game da fadin rashin shugabanci, duk wanda ya fada miki ya fadi son ransa ne kawai, domin har gobe idan wata masifar ta taso mu shugabanin dai a ke nema, kin ga shugabanci ba karya ba ne”.
Daga karshe wace shawara za ka bawa jarumai da ma sauran abokan aikin ka domin ganin Kannywood din ta daidaita, ina nufin a gudu tare a tsira tare?
“Ai ni na dai na bawa wani dan fim shawara ko wanene shi, ko kuma wane bangare ya ke ko inja hankalinsa a kan wani abu, kalma daya ce na ke fadi idan mutum ya ga dama ya ji tsoron Allah a kan sana’ar da ya ke, idan mutum ya ki jin tsoron Allah kuma gashi nan ga Allah”. A cewar Alhassan kwalle.