Kannywood

Da rufin asirina na shiga harkar fim -Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a

 Da rufin asirina na shiga harkar fim -Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a

Tsohuwa a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, wadda a yanzu ta rikide ta zama ‘yar siyasa, ta bayyana harkar fim a matsayin sana’ar da har yanzu ba ta fi karfin ta ba.

Tsohuwar jarumar, Rashida, ta bayyana hakan ne ga wakilin mu a lokacin da su ke tattaunawa da ita dangane da rashin ganin ta a cikin harkar fim, wanda hakan ya sa a ke ganin kamar ta girmi harkar fim din ne shi ya sa ba a ganin ta.

Rashida Adamu, wadda a baya ta yi fice a masana’antar, wadda kuma daga baya ta shiga harkokin siyasa, kuma har ta rike matsayin mai ba gwamnan Kano shawara a kan harkokin mata.

Da ta ke jawabi a kan tsokacin, ta ce ”Ni tun kafin na san zan samu mukami a cikin gwamnati, ka je ka yi hira da furodusoshin Kannywood, ni Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, ban taba ciniki da furodusa ba, tun da na fara fim har kawo yanzu. Kuma idan karamin furodusa ne ya zo ya na so zai yi fim ni ina zuwa in yi masa fim kyauta, saboda na tallafa masa”.

Ta kuma ce”Ni fa harkar fim da na shiga, na shiga ne domin na tallafa wa jama’a, ba wai domin na ne mi kudi ba. Saboda ni ‘yar kasuwa ce, ina da rufin asiri na. Kudin da zan samu a fim ba na tunanin su, wani lokacin ma kudin da a ka ba ni a wajen daukar fim nan take na ke ba yara na, saboda duk inda za ka ganni ba za ka ganni ni kadai ba, ina tare da mutane na ko a ina ne. To wannan kudin fim din wani lokacin ma kafin mu bar wurin daukar fim mun ci abinci da su. Ka ga kenan ni ba za a ce na raina kudin fim ba, kuma ban taba raina kudin fim ba saboda ba ma a gaba na su ke ba. Bai dame ni ba bare har na ce sai na tsawwala wa mutum kamar yaki. Abun da a ka ba ni Allah ya yi musu albarka. Idan ina ra’ayi zan iya gama maka fim sai ka dakko kudin ma na ce maka kyauta na yi maka. Kowa ya san ina yin haka a masana’antar, domin haka ni a wuri na harkar fim ta rufa mini asiri kuma ina cikin ta har yanzu ban barta ba, lokaci ne dai kawai da babu domin haka mu ka bar wa ‘yan baya”. Inji Rashida.

Sannan ta kuma yi kira ga abokan sana’ ar ta da su rinka kiyaye mutuncin junan su tare da kaunar juna domin kuwa a cewar ta, da haka ne za a samu ci gaban masana’antar, har ta zamo abar alfahari ga masu zuwa a gaba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button