Kannywood
Ana Wata Ga Wata: Karamin aiki na ne na fito zindir idan na bushi iska – Nafisa Abdullahi
Jaruma Nafisa Abdullahi ta sha alwashin yin tumbur a duk lokacin da ta bushi iska. Ta bayyana haka ne a lokacin da masu bibiyan shafin ta na Twitter suka sakata a gaba kan matun kawar ta Maryam Booth.
Tun farko dai Nafisa ta wallafa a shafin nata cewa tabbas sun san wanda ya saki Bidiyon Maryam Booth tare da bayyana cewa sai ya ɗanɗani ƙuɗar sa.
Wannan batun ne ya jawo masu bibiyan shafin ta suka yi mata chaaaa har suka kai ta ga bango.
Ga shidai daga twitter dinta.
Amma yanzu ma bai baci ba, duk lokacin da na bushi iska na zaku ganni da bikini na… ?⚖️— Nafisat Abdullahi (@NafisatOfficial) February 7, 2020
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com