Kannywood
Za a fara daukan fim ‘mafi girma’ a tarihin Kannywood
Kamar yadda Aminiya ta bayyana a rahotonta na musamman kan muhimman abubuwa guda 5 da za su dauki hankali a Kannywood, yanzu haka an fara shirin fara daukar shirin.jaridar aminiyahausa na ruwaito.
Shirin wanda Kabiru Jammaje da Abubakar Bashir Maishadda za su dauki nauyi, an bayyana Ali Nuhu a matsayin daraktan fim din.
Daga cikin jaruman fim din akwai Sani Mu’azu, da Segun Arinze da Sola Sobowale da Nancy.E.Isime da E n y i n n a N w i g w e da Ali Nuhu da Abba El-Mustapha da sauransu.
Shirin zai ci miliyoyin Naira kamar yadda masu shirya fim din suka fada, kuma an ce shi ne “fim mafi girma’ a tarihin fina-finan Kannywood.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com