Kannywood
Yanzu an samu ci gaba a harkar fim- Abba Almustapha
Daya daga cikin fitattun jarumai a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, wanda a ka dade a na damawa da shi, Abba Al-mustapha (Abba Ruda), ya bayyana ci gaban da masana’antar fina-finai ta Kannywood ta ke samu a matsayin wani babban abun alfahari ga dukkan masu gudanar da sana’a a cikin ta.
Jarumin ya bayyana hakan ne, a lokacin tattaunawar su da wakilin mu, lokacin da ya ke tambayar sa irin ci gaban da masana’antar ta samu ko kuma akasin hakan a daidai wannan lokacin.northflx na ruwaito.
Jarumin ya bayyana cewa “Ni ina ganin abun da ya fi daukar hankali na dangane da ci gaban da masana’antar mu ta samu a yanzu, abu biyu ne, ingancin labari da kuma kayan aiki, domin an samu ci gaba ba kamar yadda a ke a baya ba. Sai na ukun kuma shi ne, an samu kwarewa a cikin harkar, domin a na tafiya neman ilimi dangane da sana’ar kuma a na fadada neman hanyar kasuwancin fim da yadda zai habaka, sannan a yanzu mu na neman gwamnati ta kara shigowa cikin harkar kamar yadda mu ke ba su gudummawa, su ma su zo su ba mu ta su gudummawar. Domin a baya an ce za a yi mana Alkaryar fim, kuma abun ya zo ya samu matsala, to idan ma ba a yi mana ba, mu na so a mayar da kudin zuwa wata harka da ta shafi fim, domin kuwa duk wata gwamnatin siyasa da ta ke zuwa ta na samuwa ne tare da gudummawar ‘yan fim. Domin haka mu ke rokon su da cewa ya zama dole su zo su taimaka wa harkar fim tun da ta matasa ce da dumbin jama’a su ke cin gajiyar ta. “
Daga karshe ya ina kira ga masoya da su ke kallon fina-finan mu da su kara ba su hadin kai, wajen yakar masu satar fasaha, domin kudi mai yawa mu ke sakawa sai mu yi fina-fanai masu inganci, amma daga mun fito da shi sai masu satar fasaha su kwafa su yi mara inganci su rinka kawo muku ku na siya, domin haka ku kula ku rinka sayen mai inganci, domin ta ya mu yaki da su, domin mu kadai abun ya fi karfin mu”. Inji jarumi Abba Al-Mustapha.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com