Kannywood: Abubuwan 5 da za su dauki hankali a shekarar 2020
Kamar yadda aka sani, Masana’antar Kannywood masana’anta ce da ta ba dimbin mutane aikin yi, musamman a Arewacin Najeriya kamar yadda takwararta ta Nollywood ta ba mutanen Kudu aiki.
A shekaru kadan da suka wuce, masa’antar ta shiga matsanancin hali, inda har wasu suka fara tunanin za ta durkushe, musamman kasancewar kasuwancin masana’antar ya tabarbare.
Tabarbarewar kasuwancin masana’antar ya sa da yawa daga cikin masu shirya fina-finai suka labe, suka yi shiru kamar ba sa nan. Wasu kuma suka koma wata sana’ar, wasu kuma suka hada da wata sana’ar.
Da dama daga cikin masu shirya fim suna da fina-finai a ajiye a kasa, amma tsoron asara ya sa suka ajiye fina-finan ba su fitar ba.
Don haka ne Aminiya ta rairayo wasu abubuwa da za su dauki hankali a masana’antar a Kannywood a wannan shekarar ta 2020;
Nafisa Abdullahi za ta zama darakta
Jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa a shafinta na Instagram watannin baya cewa za ta zama darakta a karon farko.
Bayan ta shirya fim din Yaki A Soyayya, wanda ta shirya a kan matsalar shaye-shaye, kuma fim din ya yi shuhura sosai, kuma ya samu karbuwa matuka.
Sai liyafarta ta ci gaba, inda ta nuna cewa za ta zama darakta a karon farko a fim dinta mai suna Zainab Ali.
Nafisa Abdullahi ta wallafa cewa, “ina bukatar addu’o’inku. Zan zama daraktar fim a karon farko.”
Tuni mutane suka rika taya ta murna da mata fatan alheri, ciki da har Ali Nuhu da mashiryin fim, Naziru Danhajiya.
Jim kadan bayan ta yi wannan rubutun, sai ta cilla kasar waje domin karo karatu. Amma yanzu ta dawo bayan tsawon lokaci.
Yanzu kallo ya koma wajen Nafisa Abdullahi domin ganin yadda za ta kaya wajen bada umarnin fim din na ta mai suna Zainab Ali.
Banar fim din Zainab Ali da Nafisa za ta bada umarni Hoto: Shafin Nafisa na Instagram.
Bashir Maishadda da Jammaje za su shirya fim ‘mafi girma’ a Kannywood
Wani furodusa da komai wuya bai tsoron kashe kudi wajen shirya fim a Kannywood shi ne Abubakar Bashri Maishadda. Duk da cewa kasuwancin fim ya yi kasa, Maishadda ya shirya fina-finai da dama a bara, kamar su Hauwa Kulu da sauransu.
Abubakar Bashir Maishadda ya bayyana cewa shi da furodusa Kabiru Jammaje za su shirya fim mafi girma a tarihin Kannywood.
Bai bayyana yadda fim din zai zama mafi girma ba, ko kuma me ya sa zai fi girman. Sai dai ya bayyana cewa za su hada manyan jaruman Nollywood da manyan jaruman Kannywood a fim din mai suna The Right Choice. Sannan ya bayyana cewa fim din zai ci miliyoyin Naira.
Za a fara daukar fim din ne a wannan watan na Janairu.
Tun farko dama furodusan ya bayyana cewa duk fina-finan da ya shirya da kuma nasarorin da ya samu kamar sharar fage ya yi.
Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da Kabiru Jammaje
Adam A. Zango a Legas
Wani abin da masu kallo za su sanya ido su gani shi ne kasancewar jarumi kuma mawaki Adam A. Zango a Jihar Legas.
Kwanakin baya ne ya bayyana a wani hirar da ya yi da Aminiya cewa kai koma Kudu da harkokinsa, inda ya bayyana cewa zai fi mayar da hankalinsa kan wakoki, amma zai rika yin fim jefi-jefi, musamman in an bukaci ya yi.
Daga cikin abubuwan da zai fi mayar da hankali shi ne hadakar wakoki da mawakan Kudu, inda salon wakokin da yake yi suka fi tashe da samar da kudi.
A bara ne Zango ya bayyana cewa ya fice daga Masana’antar Kannywood, inda ya bayyana rashin adalci a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka sa ya fice daga masana’antar.
Masu kallo yanzu suna jira su ga yadda za ta kaya, ko Zango zai samu karbuwa a can Kudu, ko kuma zai dawo Arewa.
Farfado da Kadawood
Wani abin da kuma masu kallo za su zura ido su jira shi ne shirin farfado da Kadawood, wanda jaruman fim na Jihar Kaduna ke kokarin farfado da shi.
Bangaren Kadawood ya dade yana shirya fim, sai dai abin bai samu karbuwa yadda ya kamata, inda wasu suke cewa bai kamata a ce akwai Kannywood ba, sannan kuma a samu wani Kadawood duk a Arewa. Sannan wasu suke cewa kasancewar Kannywood ta riga ta yi karfi, zai yi wuya Kadawood ta daga har ta yi wani abun a zo a gani.
Amma dai su ’yan Kadawood suna ci gaba da kokari domin ganin hakarsu ta cimma ruwa.
Farfado da kasuwancin fim
Wannan burin duk wani mai ruwa da tsaki ne a Masana’antar Kannywood kasancewar tabarbarewar kasuwancin masana’antar ya shafi mutane da dama.
An yi taruka da dama, an kafa kwamitoci duk da zimmar ganin an shawo kan lamarin, amma abin ya ci tura.
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a masana’antar sun bayyana cewa sun shiga siyasa ce domin tunanin idan aka samu nasara za a taimaka musu wajen farfado da masana’antarsu.
A wannan shekarar, za a zura ido a gani ko hakarsu za ta cimma ruwa.
Wai da gaskene ashe hwa ?