Ba Zan yi Fim Din ‘batsa’ Ba ko Nawa za a Biyani – Sani Danja
Jaridar The punch ta zanta da babban jarumin masana’antar fina-finai kuma mawaki Sani Danja a kan lamurran da suka shafi sana’arsa. Kamar yadda aka sani, Sani Danja dai gwani ne a rawa da waka.
A yayin da aka tambayeshi wanda ya fara koya mishi rawa da waka, Danja ya ce: “Na fara rawa tun ina karamin yaro. Na kan kalla wakokin kasashen ketare tareda wasu abokaina. Daga bisani kuwa muka bude wata kungiya mai suna Musical Youths.”
Danja ya ce da farko ya fara boye zabin sana’arsa ga iyayensa amma daga baya sai suka fahimta sannan suka amince. Sun kuma ja kunnensa akan ya mayar da hankali wajen karatu don in babu ilimi babu inda ake zuwa. Saboda son cimma burinsa na zama mawaki, dole ta sa ya mayar da hankali a karatunsa.
Ya bayyana cewa Zakin Arewa da ake kiransa kuwa ya samo asali ne daga sarautar da Sarkin Nupawa, Nsi Nupe ya nada shi. Duk da tun farko ana kiransa da Zaki amma bayan an nada shi sarautar nan ne abun yafi tabbata.
Jarumin ya ce bayan sana’ar aktin, yana kasuwancinsa na siyar da motoci, yana da dakin daukar hoto da sauran kananan kasuwanci da yake yi. Ya mallaki gidauniyar tallafawa matasa kuma shi kanshi fuskar wasu kungiyoyin taimakon kai da kai ne.
A lokacin da aka tambayi jarumin a kan irin aktin din da addini ya ware, ya ce: “Addini bai fito ya bayyana irin rawar da jarumi zai taka a fim ba. Amma kuma komai na da iyakoki. Duk wata rawar da mutum zai taka da zata taba mutuncinsa toh abin gudu ne. Kamar ni babu kudin da za a bani inyi aktin din dan daudu ko na fim din batsa, ko nawa ne kuwa. Zan dai iya runguma ko sumbata a fim, na yi hakan ma kafin wannan maganar.”
Ya yi kira ga mata masu ba wa furodusoshi kansu don su yi suna. Ya ce hakan ba zai sa yin suna ba sai dai zubar da mutunci tare da lalata aikin mutum. Matukar aka nemi mace da lalata, kamata yayi ta sanar da hukumomin da abin ya shafa.