Hausa Hip Hop

Samun Hadin Kan Mawakan Arewa Shi Ne Babban Burina A Kodayaushe – Tee Swag

Tattaunawar WAKILINMU, MUSA ISHAK MUHAMMAD Tare Da MAWAKI ABDULRAHMAN USMAN, Wanda A Ka Fi Sani Da (Tee Swag).

Da Farko Za mu so ka Fada Mana Cikakken Sunanka da Kuma Takaitaccen Tarihinka.

To ni dai Sunana Abdulrahman Usman, Kuma ana kirana da Baba Pategi Samanja. Amma an fi sanina da Tee Swag a fagen Waka. Kuma ni yaron tsohon da fim din nan Samanja ne. Ni an haife ni ne a Jihar Kaduna

Yaushe Ne Ka Fara Waka?

Eh gaskiya na fara waka ne tun wajen 2005, ka ga wajen shekaru goma sha hudu (14) kenan.

Ya Ya A Ka Yi Ka Samu Kanka a Cikin Harkar Waka?

To ni dai gaskiya Daman chan tun ina dan karami Ina son harkar Waka sosai, to a haka na taso kuma har na zo na samu kaina a cikinta izuwa yanzu.

Wane Kalubale ka Fuskanta A Lokacin Da Ka Fara Waka?

Eh to gaskia abubuwan da yawa. Amma kadan daga ciki shi ne tsangwamar mawaka da wasu mutanen ke yi, da kuma wasu mutanen da su ke daukan mawaka ‘yan iska.

Wacce Ce Wakarka Ta Farko Da Ka Fara Yi?

Wakar da na fara yi ita ce wata waka mai suna “Freestyle”.

Izuwa Yanzu Wakokinka Sun Kai Kamar Guda nawa?

Gaskia bansan adadin wakokina ba izuwa yanzu. Saboda na yi su da yawa, kuma akwai wadanda na yi wasu baitoci a wakokin wasu abunda a ke cewa (collaborations). Saboda haka wakokina su na da yawa gaskiya.

A Cikin Wadannan Wakokinka Naka Wacce Waka Ka Fi So?

Wakar da na fi so a cikin wakokina ita ce wata waka mai suna “Listen to your heart”

Me Ne Ne Ya Sa Ka Fi Son Wannan Wakar?

Abinda ya sa na fi son wakar shi ne, saboda tsarin saukar baitikan wato (flaws) din wakar kai tsaye daga zuciyata su ka fito. To salon wakar ya yi min sosai, shiyasa na fi son ta.

Wacce Waka Ce Ta Baka Wahala Sosai A Lokacin Yin Ta?

Wakar da ta fi bani wahala lokacin yin ta ita ce wata waka mai suna “Baraka”

Ka Taba Fitar Da Album Ne?

Ban taba ba zuwa yanzu, amma ina nan ina aiki a kan hakan. Nan da lokaci kadan zan fitar da shi.

Me Ya Sa Ka Zabi Yin Wakokin Hip-Hop A Kan Sauran Bangarorin Waka?

Ba Hip-Hop kadai na ke yi ba, Ina yin abinda a ke cewa RnB da kuma Afro Pop.

Ka Na Yin Koyi Da Wani Mawaki Ne A Ciki Ko Wajen Najeriya?

Ni ba na kwaikwayon kowanne mawaki, ina yin Waka ne da salo na na kaina,ba na Kwaikwayon salon kowa. Wakokina ina yin su ne da salo na nishadantarwa ne. Saboda haka salona nawa ne ba na wani ba.

Wanne Irin Nasarori Ne Ka Ke Ganin Ka Samu A Cikin Wannan Harkar Taka Ta Waka?

Gaskia na samu nasarori da dama wadanda ba zan iya iyakance su ba. Kadan daga cikinsu shi ne ko a cikin shekaran nan kadai an bani (awards) guda tara. To nasarori dai kam an samu sai dai godiyar Allah.

Wane Kalubale Ka Ke Fuskanta Izuwa Yanzu?

Rashin tallafi shi ne babban kalubalen da mu mawaka mu ke fuskanta.

Wane Buri Ka Ke So Ka Ga Ka Cinma A Wannan Sana’a Taka Ta Waka?

Babban burina shi ne in ga kan mawakan Arewa ya hadu, domin ta haka ne kawai za mu yi nasarori a abubuwa da yawa.

Ya Ya Za Ka Bayyana Alakarka Da sauran Mawaka ‘Yan uwanka?

Ni ina zaman lafiya da kowa ba ma mawaka kadai ba. Saboda haka ni ba ni da matsala da kowa.

Me Ne Ne Sakonka Ga Masoyanka Masu Son Wakokinka?

Ina godiya a kan kaunar wakokina da su ke yi, da babu su da bazan zama Teeswagg ba. Kuma na yi alkawarin nishadantar da su a kowanne lokaci.

Mawaki Tee Swag Mu Na Godiya Sosai.

Ni ma na gode sosai.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button