Kannywood
Yadda Jaruma Rashida Adamu Mai Sa’a Take Shiga Lungu Da Sako Na Kauyukan Kano Tana Tallafawa Mabukata (Hotuna)
Advertisment
Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, kuma tsohuwar mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin mata, Rashida Adamu Mai Sa’a ta kasance mai tausayi da jin kan al’umma mabukata. Inda take shiga lungunu da sako musamman na kauyukan Kano tana tallafawa masara galihu a karkashin gidauniyarta ta Mai Sa’a Foundation.
Daga cikin irin hidimar da take yi wa mabukata ne, a kwanan nan Hajiya Rashida da tawagar ta suka kai ziyara wani kauye mai suna Tudun Kaba dake karamar hukumar Kumbotso, inda ta raba tallafi.
Daga cikin irin kayan da ta rabar sun hada da lesuka, atamfofi, kayan abinci, kayan amfanin gida da sauransu.
Haka kuma ta kai tallafin kayan more rayuwa ga ‘yan fursuna dake gidan yarin Goron Dutse dake birnin Kano.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com