Rashida Mai Sa’a : Mai Sa’a Charity Foundation Sun Kai Ziyarar Bada Tallafi Gidan Yari
Wannan Gidauniya Mai Albarka Karkashin Shugabar Gidauniyar Hajiya Rashida Adam Abdullahi Mai Sa’a Yau Ma Kamar Yadda Ta Saba Takai Ziyarar Rabon Tallafi Ga Bayin Allah Mazauna Gidan Yari Dake Goron Dutse A Jihar Kano
Wanda Gidauniyar Tabada Tallafin Kayaiyaki Na Amfanin Yauda Kullum Don Inganta Rayuwar Al’ummar Dake Zaune A Gidan Na Yari Wanda Yanzu Sunan Gidan Ya Koma Gidan Gyara Halaye Da Tarbiyyar Masu Laifuka
Kayaiyakin Da Gidauniyar Ta Raba Sun Hada Da…….
1.Maganin Sauro
2.Kayan Shayi Madara,Sugar,Cornflakes, Bournvita, Da Sauran Dangin Kayan Dayashafi Hada Shayi
3.Maggi
4. Manshafawa Da
5.Sabulu
Sama Da Mutanen Dari Biyu 200 Mazauna Gidan Yarin Ne Zasu Amfana Da Wannan Tallafi Da Wannan Gidauniya Mai Albarka Ta MAI SA’A CHARITY FOUNDATION Ta Bayar……………….
Shugaban Hukumar Gidan Yari Na Jihar Kano Comptroller General Nigerian Correctional Service Kano State Alhaji Ahmad Abdullahi Magaji Ya Yabawa Shugabar Gidauniyar Hajiya Amb Rashida Adam Abdullahi Mai Sa’a Bisa Namijin Kokarinta Na Ganin Ta Taimaki Rayuwar Al’ummar Dake Bukatar Taimako
Shugaban Na Hukumar Gidan Yarin Ya Jinjina Mata Matuka Tareda Karamata Karfin Guiwa Don Cigaba Da Wannan Aikin Alkhairin Datakeyi Da Addu’ar Allah Yasakamata Da Gidan Aljanna Ameen
Sakon Godiya Na Musamman Ga Jami’an Tsaron Ma’aikatan Gidan Yari Bisa Goyon Baya Dasuka Bayar Wajan Rabon Wannan Tallafi Da Fatan Allah Yasaka Musu Da Alkhairi Ameen
Sakon Godiya Da Bangajiya Ga Dukkan Members Na Wannan Gidauniya Bisa Aiki Tukuru Dasuke Don Samun Nasarar Wannan Gidauniyar Mai Albarka
Mungode
Hajiya Amb Rashida Adam Abdullahi Mai Sa’a
Shugabar Gidauniyar Mai Sa’a Charity Foundation
Ibrahim Abubakar Kuliya
SA Media And Publicity Hajiya Amb Rashida Adam Mai Sa’a