Labarai

Pantami Ya haramta Wa kamfanoni Tura Sakon Voice Mail

Ministan Sadarwa na Najeriya Dr. Isa Ali Pantami ya bai wa kamfanonin layukan waya umarnin da su daina damun masu amfani da layukan waurin tura masu sako idan an kira su ba a same su ba wato voice mail, BBC ta ruwaito.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ministan Uwa Suleiman ta fitar ta ce ministan ya fahimci cewa abin ya fara zama ruwan dare alhalin ba a saba da shi ba a Najeriya.

Kazalika mutanen da ke zaune a karkara, in ji ministan, ba sa jin harshen da kamfanonin ke amfani da shi a sakonnin sannan kuma ana cazar mutane ko ba tare da son ransu ba.
“Hakkinmu ne mu kare hakkin masu amfani da layuka a Najeriya yayin da kuma muke samar da yanayin kasuwanci ga kamfanonin layukan bisa tsarin kasuwanci na duniya,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa: “Wannan dalili ne ya sa Dr. Pantami ya umarci hukumar kula da harkokin sadarwa ta NCC da ta tabbatar cewa an bai wa masu amfdani da layukan zabin samun sakonnin bisa radin kansu ta hanyar saka wasu lambobi na musamman.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button