Malamai sun gani a mafarki cewa zan zama shugaban kasa – Sani Yariman Bakura
Tsohon gwamnan jihar Zamfara , Ahmed Sani Yarima, ya bayyana niyyar takarar kujeran shugaban kasan Najeriya kuma wasu malamai sun bayyana masa cewa an yi musu wahayin hakan. Daily NIgerian ta ruwaito.
A wata hira da tsohon gwamnan yayi a gidan rediyon Pride FM, Gusau ranar 13 ga Nuwamba, Yarima ya zayyana nasarorin da ya samu matsayin ma’aikacin gwamnati da dan siyasa.
Yarima ya bayyana cewa ba zai sake wani takaran wani kujera a jihar ba, babban burinshi daya ne yanzu; gadar kujeran shugaba Muhammadu Buhari a 2023.
“Na gama takara a jiha, amma tabbas zanyi takarar shugaban kasa. Tuni wasu manyan yan siyasa da Malamai suna aikin ganin an cimma wannan manufa.”
“Ko a daren jiya, daya daga cikin Malaman ya kira kuma ya rantse cewa ya gan ni cikin mafarki na zama shugaban kasa, cikin motar shugaban kasa.”
“Nima Sai na fada masa wani labari mai alaka da hakan da wani tsohon abokin makarantan sakandare na wanda ya kasance tsohon kwamishana a lokacin gwamnatin Mamuda Shikafi ya fada min.”
Ya fada min cewa “Wani balarabe ya bayyana gabansa a Harami, ya gaishe da shi kuma ya ce daga gani kai dan jihar Zamfara ne.”
“Sai ya tambayesa ‘Ina babanmu Sanata Ahmad Sani Yeriman Bakura? Sai abokin ya fada masa cewa ina nan lafiya.”
“Sai ya ce masa ya isar da gaisuwarsa gareni sannan ya fada musu cewa idan Allah ya yarda, zan jagoranci Najeriya, sai dai idan na mutu.”
“Sai mutumin ya tafi. Yayinda suke kokarin wucewa, sai matar abokina ta bada shawaran cewa a tambayi shi (Balaraben) sunansa saboda saukin isar da sakon.”
“Abinda ya basu mamaki, mutumin ya bace, sun nemeshi sun rasa.”
“Da abokin nawa ya fadawa daya daga cikin malamansa abinda ya faru, Malamin ya fada masa cewa wahayi ne Allah ya aiko.- a cewar Yariman Bakura