Kannywood

Harkar Fim ce ta sauya min Rayuwa – Fati Shu uma

Northflix ta ruwaito,Daya daga cikin fitattun jarumai mata da su ke jan zaren su a cikin masana’antar finafinai ta kannywood mai suna Fati Abubakar Wacce aka fi sani da Fati Shu’uma, ta bayyana harkar fim a matsayin wata harka wadda ta sauya mata rayuwa zuwa ingantacciya.

Jarumar ta fadi haka ne a lokacin da su ke wata tattaunawa da wakilin mu dangane da nasarorin da ta samu a cikin masana’antar kannywood in da take cewa “Gaskiya na samu sauyin rayuwa, wadda ban taba za to ba.

Sauyin da na samu a rayuwa ya sa ba ko ina na ke shiga ba saboda sanin fuska ta da akayi. A da ina iya shiga ko ina na yi mu’amala da jama’a, amma yanzu duk inda na je sai a rinka nuna ni. Domin haka har Nikabi na ke sawa a wasu lokutan.” In ji Shu’uma

Mun tambaye ta irin kalubalen da ta samu tun shigar ta harkar fim?

Sai ta ce

eh zan iya cewa na samu kalubale kwarai a gaskiya, domin tun da zan shigo harkar  nake zuwa ganin yadda ake daukar fim. Na fara zuwa wajen daukar wani fim mai suna GANI GA KA, lokacin sai mahaifina ya rufe ni da fada ya ce domin me zan je.

Ka san yadda mutane su ke daukar harkar fim. Shi ya dauka zan je na tare a gidan karuwai ne amma daga baya sai ya fahimci ba haka bane.” Inji Jarumar

Yanzu kin zama babbar jaruma ko me ya fi burge ki a cikin harkar fim?

Abin da ya fi burge ni shi ne yadda na ke gudanar da rayuwata cikin sauki, kuma ni daman ba ni da wani babban buri na rayuwa,  Domin haka komai nawa ya ke tafiya cikin sauki, ka san idan mutum ya dauki rayuwa da zafi, sai abin ya zo ya yi ta damun sa, to ni ban dauki rayuwa haka ba, domin haka har kullum nake alfahari da harkar fim.

kuma ina kallon kaina a matsayin wadda ta shiga harkar fim a sa’a domin lokacin da na shiga ban dauki lokaci mai tsawo ba aka yi mini fim mai suna “SHU’UMA” kuma na zamo Jarumar fim din, kafin wata biyu sai ya zama duk inda na shiga ana kira na da Fati Shu’uma, ka ga ba kowacce jaruma ba ce take samun wannan sa’ar.”

Daga karshe ko wanne buri Fati Shu’uma ta ke da shi dangane da harkar fim?

To ni dai babban buri na dai a yanzu shi ne na samu miji na yi aure, don haka ina ta addu’a Allah ya kawo mun miji nagari Wanda za mu yi daidai da juna, zai fahimce ni, nima na fahimce shi, ta yadda za mu yi zaman aure na fahimtar juna.” A cewar Fati Shu’uma

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA