Kannywood

Aminu Abubakar Ladan Alan Waka Ya Zamo Sarkin Wakar Sarkin Dutse

Masha Allah Shahararren mawakin a kasar hausa wato Aminu Abubakar Ladan Alan waka wanda Sarkin Dutse ya Nada shi a matsayin sarkin wakar sarkin dutse.

Wanda yayi rubutu mai hikima da godiya bisa Wannan sarauta da ya samu.

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki abisa dacewa da cancanta. Madauwami da daukaka mafificiya abisa iko da sarrafawa.
Daga matsayai na daraja dangin Shuhura da daukaka da martaba da mutunci tare da budi, babu abinda zamu cewa Allah sai Jimlar: ALHAMDU LILLAHI RABBUL ALAMINA.
Game da Sarauta da mutane suke ji da gani, matsayi ne da ke da matakai na gado ko Zawarci na bukatar mai nema da wanda ake nema da Rawani. Wanda bai gaji Sarauta ba kuma yake neman a bashi sarauta, Rubutawa yake ko ya je ya fadi yai gaisuwa don neman matsayi na Sarauta. Sai a duba cancanta tare da shawarar majalisa ko ra’ayin Sarki bisa Sahalewar Gwamnati sai a bashi Sarauta.
Masarautar BICHI da Masarautar DUTSE Ni Aminu Ala ‘Da ne halastacce wanda zai iya kama kan bare ya kai a nada masa Rawani ba ni kaina ba. Ina mamaki ta yarda Masoyana suka Afu da Son ganin Samun matsayin Sarauta agareni, kamar wata babbar dama ce ta daukaka ko tawaya idan ba a bani Satauta ba. Na sani soyayya ce da kishi, irin na kauna da girmamawa ta sa Mutane ke kama kaina su nada min rawani da sunan sun karramani a Idon Duniya. An yi min Haka karkashin Sallaman Maimartaba Sarkin Kano 45 Annivasary, An yi min haka a FCE Zariya an yi min haka A bikin Yayan Sarkin Kano Ado Bayero Salisu da Badde, an yi min haka Ranar Mawakan Hausa Foundation a kaduna da Jigawa. An yi min haka a Masarautar Bichi karkashin Jagorancin Dan Sarki Sanusi I Alh. Isa Pilot a gaban Mai Martaba Sarkin Bichi Alh. Aminu Ado Bayero. Yau Kuma ranar da ta zo daidai da 8/11/2019. An yi min haka a Kasar Dutse a yayin Deaner ta kaddamar da ayyukan Foundation na NHD Foundation. Hakika dukkan abinda ya faru akan wadannan nade-nade, babu wanda aka taba yinsa da Masaniyata ko neman izinina, haka mutane ke ganin dacewa su aiwatar don karramawa agareni shi ne farin cikinsu, kuma nima ina matukar jin dadi da hakan.
Sai dai Ina so masoyana su Sani. Kowanne Mahaluki yana da irin baiwarsa ta Daukaka da martaba mai tasirantuwa izuwa ga mutane. Ku taya ni godewa Allah da Irin Baiwar da yayi mani wacce a wannan Zamani banga mai Irinta ba.  Wakoki irin na Aminu Alan waka basa bukatar Mukamin Sarauta ko na mulki. Allah ya jagorance mu fadin gaskiya da binta.”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button