Labarai

MINISTA SHEIK PANTAMI YA KAFA TARIHI : Cikin Kwanaki 45 Ya Yi Ayyukan Da Aka Gagara Yi A Tsawon Shekaru Bakwai 7

Maigirma Ministan sadarwa na Ash-sheikh Dr Isa Ali Ibrahim Pantami yace;  “a cikin kwanaki 45 da na zama Minista, mun yi nasaran magance wasu manyan matsaloli a ma’aikatar sadarwa wanda tsawon shekaru bakwai aka gagara magance su…”

Ministan ya yi wannan jawabin ne a yau Alhamis 3-10-2019 lokacin da yake ganawa da wakilin Bankin Duniya Mista Shubham Chaudhuri a Abuja.

Dr Isah Ali Pantami ya kara da cewa; “Lokacin da nazo na bada umarni cewa a rufe duk layukan da ake amfani dasu wadanda ba’a musu rijista ba kusan miliyan goma, a lokacin kamfanonin layukan wayan sunyi ta neman su gana da ni, amma naki amincewa, nace babu wanda zai gana da ni har sai sunyi abinda ya dace, yanzu anyi nasaran dakile wasu matsaloli a harkan sadarwa..” inji Ministan

Alherin Allah Ya kai ga Maigirma Ministan Ministoci Ash-sheikh Dr Isah Ali Ibrahim Pantami, yanzu a Nigeria kamar babu wani Minista sai Ministan Sadarwa, shi kadai ake jin duriyarsa saboda ayyukansa na alheri

Muna rokon Allah Ya cigaba da yiwa Malam jagoranci
Allah Ka bashi nasara, Ka sa ya wanye lafiya. Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

Daga Datti Assalafiy

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button