Labarai

Hotuna: Murna Ta kaure Yayin Da Hauwa Indimi Da Mijinta Dan Gidan Marigayi ‘Yar’Adua suka Haifi Wani kyakkyawan Yaro

Bayan shekara daya da auren su, Allah ya albarkace su da kyakkyawan jariri namiji

– Hauwa Indimi da Mijinta Mohammed ‘Yar’Adua sun samu karuwar ne a jiya Laraba 2 ga watan Oktobar nan

– Hauwa ce dai ta sanar da samun karuwar ta su a shafinta na Instagram, inda ta sanya hotonta rungume da jaririn

Hauwa Indimi, diya a wajen hamshakin mai kudin nan na garin Maiduguri, Mohammed Indimi da mijinta Mohammed ‘Yar’Adua, dan gidan marigayi tsohon manajan kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Allah ya albarkace su da samun karuwar haifar kyakkyawan jariri namiji.

Hauwa ce ta bayyana wannan labari a shafinta na sada zumunta na Instagram a jiya Laraba 2 ga watan Oktobar 2019 dinnan. Ta sanya hotonta a lokacin da take rike da jaririn a hannunta, inda tayi rubutu kamar haka:

Hauwa and Baby
Alhamdulillah, Allah ya albarkace mu da tsalelen yaro.”

Idan ba a manta ba Hauwa da mijinta Mohammed ‘Yar’Adua sun angwance shekarar da ta gabata, inda aka sha shagalin biki.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button