Kannywood

Farida Jalal Ta Dawo Fim Ne ?

Duk A Cikin Shirin ‘Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Da alama dai a yanzu yayin dawowar tsofaffin jarumai a cikin masana’antar finafinai ta kannywood ake yi, wadanda suka ci zamanin su a baya kuma yanzu ma suke kara dawowa da tunanin za su kara cin duniyar su da tsinke ba tare da la’akari da yadda masana’antar  take ba a halin yanzu.

Farida Jalal tana cikin tsofaffin jarumai da suka ci zamanin su a baya wadda a cikin shekarar 2002 kusan babu wata jaruma da take tashe kamar Farida Jalal, kafin daga baya harkar ta ajiye ta, ko da yake za a iya cewa hayaniyar Hiyana ce ta taba ta a 2007 lokacin da aka kori wasu daga cikin ‘yan fim cikin su kuwa har da Farida Jalal, tun daga nan dai aka daina ganin ta a cikin harkar fim, sai daga baya ne ta auri wani malami in da har suka samu haihuwa a tsakanin su, amma dai daga baya auren ya mutu don haka sai ta koma gida Katsina da zama.

A yanzu dai za a iya cewa Farida Jalal ta dawo cikin ‘yan fim don kuwa jefi-jefi ana ganin ta a wajen lokeshin, kuma a kwanan nan an yi wani aikin  fim da ita a Kano, akwai Kuma wakokin da za su fito nan gaba kadan wadanda ta fito a cikin su.

Abin da mutane suka dade suna tambaya shi ne wai me ya sa ‘yan fim komai dadewar su da barin harkar fim duk lokacin da suka samu dama sai sun dawo? Shin wani asiri ake yi musu ko Kuma harkar tana shiga cikin Jini ne?

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button