Labarai
An Gano Wanda Aka Nuno A Wani Bidiyo Yana Rawa Aka Ce Sheikh Daurawa Ne
Mutumin mai suna Abubakar Terab ya fito ya tabbatar da cewa shine da matarsa suke rawa, a yayin auren wani abokin sa.
Shi ma angon Muhammad Yusuf dake garin Maiduguri ya tabbatar da cewa a yayin auren sa ne aka dauki bidiyon.
Angon ya kara da cewa an daura auren ne a ranar 14 ga watan Satumba 2019 a yankin White House Arena dake garin Maiduguri.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com