Uncategorized

Yadda Kananan ‘Yan Mata Suka Maida Kawunansu Karuwai Gida

Tonga Abdul

Ana kiransu Home Girls. Sune ‘yan mata kanana da ko auren fari basu yi ba. Suna zaune ne a gaban iyayensu ko kuma wasu ‘yan uwansu. Amma ta’asar da suke tafkawa yafi na karuwan da suke tsayiwuwa a titi suna jiran abokin zinan da zai zo a daukesu.
Akasarin wadannan ‘yan matan suna karatu kodai a Koleji ko kuma a jami’a. Suna da wayewa irin na zamani ba jahilai bane mafi yawansu.
Yadda suke gudanar da aiyukansu na karuwanci shine. Kowacce tana da manajanta ma’ana kawalinta. Wanda yake yawo da hotunanta a wanyansa. Da yake masu sa’anar kawalanci suna da masu neman matan yin zina a wajensu don haka cikin sauki suke tallatasu kuma su samu shiga wajen masu bukatarsu.
Zaka yi mamaki idan kaga irin wadannan ‘yan matan suna gudanar da harkarsu na karuwancin gida. Domin Sam basu yi kama da masu wannnan dabi’ar ba. Yarane a fuska da shekaru, kuma suna da kamala a dabi’ance. Jikinsu babu alamun wahala ko yunwa bare rashin gata.

Na gano irin wadannan karuwan gidan ne dalilin wani abokina. Saboda shi duk garin da zai shiga a fadin Arewacin Nijeriya yanada kawalin da zai hadashi da irin wadannan yaran. Ko kuma cikin ‘yan matan da yake mu’amalan zinan dasu su hadashi da wata kawarsu da suke irin wannan bakar sana’ar tare.
Na tambayeshi dalilinsa na kula irin wadannan ‘yan matan da kusan yayi jika dasu. Amsarsa bai wuce shi mai sha’awar kananan yara bane. Kuma Hulda da irin wadannan matan da akwai rufin asiri ganin ba gidajen karuwai take zuwa ba. A cewarsa yana kwance a dakin hotel dinsa suke shigowa su kawo masa.
Ya kara da cewa shi bayason amfani da kwaroron roba haka kuma yake ga yawancin irin wadannan kananan karuwan gidan basu son ayi mua’amala dasu na zina da roba.
Gaba daya hujjojinsa basuda makama a wajena nayi ta mamakin a duk lokacin da zanga wata tare dashi.
A kwai wata rana da yazo naje otel dinsa mu gaisa. Naga wata ‘yan mata ba zata wuce shekaru 18 zuwa 19 da haihuwa ba. Kyankyawa tamkar iyayenta sunyi shawara da Allah kamin su haifota. Tanada natsuwa, kayan jikinta sunfi kudin kayan dake cikin jakar mazinacin nata. Fara sul. Muka gaisa har zan fita sai abokin nawa ya bukaci na sauke ta a unguwarsu saboda ita bata kwana waje. Hakan ne ya bani damar saninta sosai da abunda yasa take karuwancin gida.
Tace bata sanshi ba kawalinta ne ya hadasu. Kuma wannan shine mutum na biyar da yake hadata dasu, kuma shine talaka a cikinsu. Tace biyu gwamnoni ne suka yi zina da ita ta fadamini sunansu kuma ta nuna mini hutunanta dasu wanda bata sani ba na tura wayana. Biyu kuma basarake ne da kuma wani Sanata sai wannan abokin nawa cikon na biyar dinsu kuma a cikin watanni biyu tayi wannan mu’amala.
‘Ni gaskiya da farko kawai kadaici ne na gaji da zama gida ni kadai bayan dana dawo hutu gida daga jami’a. Akwai wata kawata datake irin wannan ita ta hadani da manajan na tura masa hutunana bayan mako guda ya tambayeni idan zan iya zuwa Lagos na samu Gwamna………. Nace masa matsalar bazan iya kwana a wajen bane. Amma zan iya fita daga 8 na safe zuwa 8 na dare babu damuwa. Bayan ya sanarwa Gwamnan yace ba matsala koda away biyu zanyi. Suka tura mini ticket zuwa da dawowa. Ina sauka a direba ya dauki sai otel. Ban wuce awa guda na sai Gwamna yazo muka yi hira hudu na yamma aka dawo dani airport 6:30 ina gida. Abunda ya bani na turawa manaja nashi yaji dadi. Ni ba waima saboda kudin naje wallahi. Kawai dai ina sha’awane kuma ko ba komai na hadu da mutane su debe mini kewa. Kaga gidanmu, ka san mahaifina a garinnan”. Kunji hairan danayi da wannan budurwar gidan kuma ‘yar wani babban mutum ne a garin Kaduna.
Naci gaba da haduwa da irin wadannan ‘yan matan ta hanyar abokin nan nawa kuma babbane a gwamnatin jiha. Kowacce da dalilinta na shiga karuwanci a gaban iyayenta. Wasu suce kudin makarata, wasu rayuwa ya musu tsauri. Wasu sha’awa wasu kuwa iskancine kawai a cisu a basu kudi ko ayi yamotsi.
Akwai wata ‘yar shekaru 16 da nasan wanda yake shirin aurenta har an kai kudin amma bashi, itama bata kwana amma daga karfe 6 zuwa 8 take zuwa yace kuma duk da kankantar shekarunta tafi yawancin matan da yake zina dasu hazama. Domin idan bai shirya bama baya gayyatanta. Shi kuma saurayin nacan yana ta surutun zai auro karamar mace wacce batasan namiji ba.
Babu abunda yafi garemu mu iyaye da muke da ‘ya’ya da kuma kanne irin my dukufa da addu’ar Allah Ya shirya mu Ya shirya mana zuri’a, masu wannan badalan mazansu da matansu irin abokina wane Allah Ya shiryesu

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA