Labarai

Mahaifiyata Ta Tsine min Saboda Na Koma Addinin Musulunci – Matashiya

Shafin legit ya samu labari ,Wata ma’abociyar amfani da sandalin sada zumunta na Tuwita (@ayushadeyah) ta bayyana yadda ta koma addinin Musulunci amma ta shafe tsawon shekaru 5 kafin ta sanar da mahaifiyar ta
– Ayushhadeyah ta ce mahaifiyata ta tsine mata a karo na farko bayan ta kira ta domin sanar da ita cewa ta zama Musulma
– A cewar matashiyar, daga baya mahaifiyarta ta zo ta hakura bayan ta fahimci cewa babu abinda zai hana ta cigaba da zama a cikin addinin Musulunci
Wata ma’abociyar amfani da dandalin sada zumunta na Tuwita mai lakabi da @ayushadeyah ta bayyana yadda ta koma addinin Musulunci amma ta shafe tsawon shekaru 5 kafin ta sanar da mahaifiyar ta.
A yawancin al’adun Afrika, mace na koma wa addinin mijinta bayan sun yi aure, lamarin da yasa @ayushhadeyah ta iya rike sirri na tsawon shekaru biyar ba tare da sanar da mahaifiyarta cewa ta canja addini ba.
Matashiyar ya bayyana cewa ta kasa sanar da mahaifiyarta ne saboda tana tsoron yadda mahaifiyarta zata ji idan ta fada mata. Ta kara da cewa amma daga baya wata kawarta ta bata shawarar cewa ta cire tsoro, ta sanar da mahaifiyarta gaskiyar zance.
Ayushhadeyah ta ce mahaifiyarta ta ji matukar jin ciwon labarin cewa ta koma addinin Musulunci, musamman ma yadda ta boye mata gaskiyar zancen har na tsawon shekaru biyar.
A cewar ta, “mahaifiyata ta ji matukar ciwon jin labarin, a cikin kuka ta dinga yi min tambayoyin me tayi min da zan yi mata haka tare da fada min cewa zan iya saka mata guba tunda har na iya boye mata maganar na canja addini na tsawon shekaru biyar.”
Mahaifiyar matashiyar har tsine mata sai da tayi tare da yi mata kashedin cewa kar ta sake cewa ita ta haife ta, amma, matashiyar ta ce ta shaida wa mahaifiyarta cewa zata cigaba da yin addinin duk da haka.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA