Alherin Allah Ya Kai Ga Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami (karanta)
Maigirma Ministan sadarwa na Kasarmu Nigeria Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya rubuta wasika zuwa ga Maigirma Ministan Ayyuka na Kasar Nigeria Babatunde Fashola yake tunatar dashi manyan ayyukan gina titi da ake yi a mahaifarsa na jihar Gombe kamar haka:
-Hanyar Gombe zuwa Potiskum
-Hanyar Gombe zuwa Biu
-Hanyar Gombe zuwa Dukku
-Hanyar Gombe da ta tashi zuwa Yola
Maigirma Ministan yayi kira ga takwaransa Ministan ayyuka da ya kai agajin gaggawa game da gyaran wadannan hanyoyi da sukeyin tafiyar hawainiya
Ina mutanen Gombe da suka nuna adawa da hassada lokacin da shugaba Buhari ya fitar da sunan Malam Isah Ali Pantami cikin wadanda zai basu mukamin minista?
To kunga kyakkyawan yunkurin da Malam yake yi domin cigaban jihar Gombe
Muna fata a nan gaba Gombawa zaku zabi Malam a matsayin gwamna
Yaa Allah Ka daukaka darajar Malam Isah Ali Ibrahim Pantami