Yabon Gwani Ya Zama Dole : Shugaba Buhari ya jinjina wa wani gwamnan PDP
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara
– Hakan ya biyo bayan tsayawar da gwamnan yayi wajen ganin ya wanzar da zaman lafiya a jihar
– Buhari yace Matawalle ya nuna kishi sosai akan jiharsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jadadda cewa ya zama dole a fito fili a rika jinjina wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle saboda jajircewar da yayi wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan yankin Arewa da suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa karkashin jagorancin sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar III a jiya Juma’a, 23 ga watan Agusta.
Shugaban kasar yace: “Ina kira ga gwamnatocin jihohin kasarnan da su yi koyi da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kan yadda ya maida hankali wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar Zamfara da kuma irin matakan da yake bi domin samun nasara a kai.
“Matawwalle ya nuna kishi matuka da son zaman lafiya a jihar ta hanyar hada kan mutanen jihar.”

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




