Karanta Martanin Mutane : Zan Iya kare Rayuwata Ba Tare Da Ɗa namiji Ya kusance Ni Ba – Najwat
Wata budurwa ta bayyana cewa za ta iya rayuwa ba tare da ta kusanci naamiji ba har ta mutu.
Budurwar mai suna Najwat ta bayyana hakane a shafinta na Facebook.
Wannan magana ta budurwar ta kawo kace-nace matuka a shafukan sadarwa.
Wata budurwa mai suna Najwat ta bayyana cewa za ta iya rayuwa ba tare da da namiji ya kusance ta ba.
Najwat ta bayyana hakan a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa na
Facebook, inda ta ce
“Bai zama dole sai da namiji zan rayu ba, domin kuwa ina ji a raina zan iya rayuwa ba tare da da namiji ba.”
Wannan rubutu da budurwar ta wallafa ya kawo kace nace matuka a shafukan sada zumunta, inda mutane suka dinga mayar mata da martani kala-kala akan wannan rubutu da ta wallafa.
Wata mace mai suna Maryam Abdu Ali tayi sharshi akan maganar budurwar ta ce:
“Dole mace ta yarda za ta rayu da namiji haka shima namiji mutukar ana so aga daidai, tunda Allah ne ya tsara hakan, saboda haka na kalubalance ki ‘yar uwa matukar kina da lafiya.”
Shi kuma wani namiji mai suna Ashraf Abdullahi cewa yayi:
“Cikin abubuwa uku watakila tana fama da daya, na daya ko tana da iskokai, na biyu ko bata da lafiya, na uku ko kuma tana mu’amala da mata ‘yan uwanta ne.”
Shima Aminu Turaki cewa yayi:
“Ina jin ke ‘yar madigo ce, amma ki sani maza rahama ne a gareku haka muma ku rahama ne a garemu dole in dai ke cikakkiyar Musulma ce to ki yadda da cewa dole kiyi aure har kiyi rayuwa da da namiji kuma ki haifi da namiji.”