Labarai

Da dumi dumi: Buhari zai kwace NEPA daga hannun yan kasuwa, zai mayar musu da kudinsu

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar sake kwato kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya, wanda yan Najeriya suka fi sani da tsohon sunansa ‘NEPA’ daga hannun yan kasuwa don ceto Najeriya daga matsanancin matsalar wuta da ake fama da shi.

Wannan mataki da gwamnati ke shirin dauka ya zo ne a daidai lokacin da za’a gudanar da cikakken nazari na karshe game da ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki watau DISCOS, don tabbatar da ko suna aikinsu yadda ya kamata ko kuwa a’a.

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito gwamnatin Najeriya za ta biya yan kasuwan da suka mallaki kamfanonin rarraba wuta guda 10 naira dala biliyan 2.4 a matsayin kudin fansa, kimanin naira biliyan 736 kenan.

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa ma’aikatar ayyuka, wutar lantarki da gidaje ta bayyana kamfanonin guda 10 a matsayin asararru, wadanda ba zasu iya kawo cigaba a harkar wutar lantarki a Najeriya ba.

A ranar 1 ga watan Nuwambar 2013 gwamnatin tsohon shugaban kasa Goolduck Jonathan ta sayar da hukumar wutar lantarkin Najeriya ga yan kasuwa bayan ra fasata gida uku, bangaren samar da wuta, bangaren dakon wuta da kuma bangaren rarraba wutar, amma har yanzu bangaren dakon wutar na hannun gwamnati ne.

A cikin makonnan kadai, an samu koma baya a adadin wutar lantarkin da Najeriya ke samu, daga megawatt 3,264 a ranar Litinin zuwa megawatt 2,842 a ranar Alhamis, wanda hakan ya kara jefa Najeriya cikin duhu.

Haka zalika gwamnati ta zargi kamfanonin da kin samar da isashshen jari don amfani dashi wajen samar da wutar lantarki, a dalilin haka an kulle tashoshin wutar lantarki guda 17 cikin 27 saboda rashin sayan wutar da suke dashi a kasa.

Idan za’a tuna a watan Yulin shekarar 2015 ne gwamnati ta amshe kamfanin rarraba wutar lantarki na yankin jahar Yola, mai suna Yola Disco, sakamakon masu zuba hannun jari a kamfanin sun janye saboda matsalar tsaro a yankin Arewa maso gabas, sai dai har yanzu gwamnati bata biyasu kudinsu ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button