Labarai

Da Alamu An Soma Samun Fahimtar Juna Tsakanin Darika Da Izala (Hotuna)

…saura a soma sallah a masallaci daya

Ana ta zumunci tsakanin jagororin Darika da Izala a kasar Saudiya, wanda hakan yana nuna alamar cewa ana samun fahimtar juna da hadin kai a tsakanin bangarorin guda biyu a Saudiya.

To ya kamata idan an dawo Nijeriya bangarorin biyu su hallatawa juna yin sallah a masallatan juna, ya zamo duk inda salla ta kama musulmi yayi salla ba lallai sai a masallacin kungiyarsa ba, domin yin hakan shi zai samar da tabbatacen zaman lafiya da hadin kai tsakanin bangarorin biyu.

Mu a bangarenmu yan darika mun yarda duk mai fadin Lailaha Illa Lahu musulmi ne ba lallai sai yana darikar Tijjaniyya ko kadiriyya ba, saboda haka idan ana son zaman lafiya mai daurewa dole ne kowace bangare ita ma ta yarda duk mai fadin Lailaha Illa Lahu musulmi ne ko baya bangaren ta.

Allah ya kara hadan ka musulmi akan tafarkin Manzon Allah SAW.

Daga Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria (Mataimakin Shugaban Kungiyan Fityanul Islam Ta Kasa)

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button