An Kaddamar Da Kwamitin Yi Wa ‘Yan Fim Rijista A Kano Domin Tsaftace Masana’antar
Shugaban hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano Malam Islamil Na Abba Afakallah, a jiya Litinin ya jagoranci taron duk masu ruwa da tsaki na masu harkokin sana’ar finafinan Hausa da mawaka. Inda ya kaddamar da kwamitin tantancen masu shirin finafinai da masu waka domin tsaftace harkar tare da inganta ta domin cigaban jihar Kano.
Yayin kaddamar da kwamitin Afakallah ya yi kira ga duk masu sana’ar finanfinan Hausa da mawaka ya zama dole su yi rijistar domin a tantance su.
Bijirewa wanan umarni kowaye mutum zai fuskanci hukuncin dokar da hukumar ta tanadar tun shekarar 2001.
Kuma hukumar tana maraba da sabbin Matasan Jahar Kano da suke sha’awar wannan sana’a da su hanzarta zuwa hukumar dake ARTV domin ‘yan wannan kwamiti su yi masa rijista