Labarai

Abin Boye Dai Yana Kara Fitowa Fili : Sheikh Abduljabir Wajen Taron Yan Shi’ah A Kasar Iraq (Hotuna)

Rubutawa: Anas Assalafiy Fagge.

Tin wasu shekaru a baya da Mln Abdul-Jabbar shehi Nasiru Kabara ya dauko tallan shi’anci a cikin rigar Qadiriyya muke ta kokarin haskawa al’ummar Annabi Alaihis-salam, tin da farko ya fara da sukan Yazidu dan babban sahabi Mu’awiya (R), a lokacin Yana yabon Mu’awiya (R), sai ya dawo sukan Shi sahabi Mu’awiya (R), yanzu abin yakai har su matan Annabi Alaihis-salam yake tabawa ya ci mutuncin su bayan su Sayyadina Abubakar da Umar da sauransu.

Amma kullum sai makafin yaran shi da yake yaudara su ringa cewa ba dan Shi’a bane madugun nasu, kawai dai kaunar Ahlul-Baiti ce, sun manta farkon wadanda suke fara amsa Sunan Ahlul-Baiti sune matan Annabi Alaihis-salam.

To yanzu dai a hankali gashi gaskiya tana Kara fitowa.

Ga Malam dan tamore a bikin Gadeer kum na ‘yan Shi’a da sukeyi duk shekara.

Allah muke roko idan Mai shiryuwa ne ya shirye shi, ya shiryi wadanda yake ja ido rufe su gane gaskiya, ya Kara tabbatar damu akan shiriya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button