Uncategorized

Wata matar aure ta nemo wa mijinta mata ta biyu yayin da ta dauki juna biyu

Ko a cikin litattafai da finafinai, ana nuna kishin mutane a kan wanda suke so, musamman a irin zamantake wa ta aure ko soyayya.

Amma duk da hakan sai gashi an samu wata mata a kasar malaysia da ta yi zarra ta hanyar nema wa mijinta mata ta biyu da zata kula da shi yayin da juna biyun da ta dauke da shi ya yi nauyi.

Matar, Khuzatu Atiqh, ta kasance tare da mijinta, Samuel Dzul, tun 2011 kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

A cewar rahoton da jaridar ‘Asia One’ ta wallafa, Atiqah ta tsinci kan ta cikin yawan laulayi lokacin da take da cikin yaronsu na biyar.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta (Facebook), Atiqah ta bayyana cewa rashin lafiyar ta tayi tsananin da sai a kujera ake tura ta. A cewar ta, “na kasance cikin damuwa a kan halin da miji na da yaran mu zasu shiga idan wani abu ya same ni.”

Rahoto daga legit ,a cikin wannan yanayi ne Atiqah ta yanke sawarar fara nema wa mijinta mata ta biyu, wacce za ta iya kula da shi da ‘ya’yansu, kuma a dandalin sada zumunta ne Atiqah ta gano wata mata mai suna Nur Fathonah, wacce daga bisani ta gamsar da mijinta cewa ya kamata ya aure ta a matsayin mata ta biyu.

Atiqh ta sha fama da Fathonah kafin daga bisani ta amince ta zo gidansu domin su karya tare, sannan ta gabatar da ita ga mijinta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA