Labarai

Siyasa Ba Gaba Ba: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Tura Wa Dino Melaye Sakon Ta’aziyya

Advertisment

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sakon ta’aziyya ga dan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye.

Sanatan, wanda ke karkashin tutar jam’iyar PDP kuma me yawaita suka ga salon mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyar APC, ya rasa mahaifiyarsa, Deaconess Comfort Melaye, a watan Mayu.

A wata wasika da ya sanya wa hannu, Shugaban Kasa Buhari ya yi wa Dino Melaye da dukkan sauran iyalan gidan Melaye ta’aziyyar mutuwar mahaifiyar sanatan mai suna Deaconess Comfort Melaye (JP).

Advertisment

Shugaban kasa ya yi wa sanatan kalamu masu dadi da saukaka zuciya tare da nasiha a gare shi kan ya yi koyi da irin halayyarta ta sadaukarwa da hidima ga Ubangiji da al’umma. Ya kuma yi masa addu’ar samun hakuri da juriyar rashinta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button