Labarai

Shin Ko Kunsan Waye Silent Billionaire?

Daga Sabiu Danmudi Alkanawi.

Shine Alh Abdussamad Isyaka Rabiu CON. Wanda akewa lakabi da ‘silent Billionaire’ saboda rashin kwakwazonsa a kafofin yada labarai.

An haifeshi a jihar kano, a gidansu dake Dala a shekarar 1960. Mahaifinsa Mal/Alh Isyaka Rabiu attajirin dan kasuwa ne, kuma malami ne, mai rike da shugabancin darikar tijjaniyya ta Afirka.

Anan kano Abdussamad yayi karatun allo, firamare da kuma sakandare, daga bisani ya samu tafiya jihar Ohio ta Amurka, wata jamia mai suna Capital University Columbus inda yayi digirinsa.

Ance ya dawo kasar Najeriya yana da shekaru 24 da kammala karatunsa, a wuraren shekara ta 1984 lokacin da Shugaba Buhari ya daure mahaifinsa a mulkinsa na soja na farko bisa zarginsa da boye shinkafa.

A wancan lokacin ne Abdussamad ya cigaba da tafiyar da harkokin kasuwancin mahaifinsa.

Attajiri Abdussamad ya kafa kamfanin BUA a shekarar 1988, wanda a lokacin ya soma safarar shigo da shinkafa da kayan masarufi, da kuma tama da karafa.

Masu ruwaito tarihinsa sunce ya soma samun gagarumar Nasarar kasuwanci ne a lokacin da wani kamfani Mallakin gwamnati mai suna ‘Delta Steel Company’ ya bashi kwangilar shigo da kayayyakin sarrafa tama da karafa da yake bukata, inda shikuma ya biya kwangilar da ma’adinan kasar nan tayadda attajirin ya fita dasu ya siyar.

Ai kuwa shekaru kadan da haka kamfanin BUA ya Mallaki Kamfanin samar da man gyada mai suna Nigerian Oil Mills, daga bisani kuma ya kafa kamfanonin samar da fulawa a lagos da kano a shekarar 2005.

A shekarar 2008 ne kamfanin BUA ya soma gogayya da rukunin Kamfanin Dangote wajen soma samar da sukari a kasar nan, daga nan kuma ya soma fadada hannun jarinsa a kamfanin samar da siminti mai suna Northern Nigeria cement company.

A shekarar 2015, Attajiri Abdussamad Isyaka Rabiu CON ya sanya hannu da wani kamfanin kasar sin domin kafa katafaren kamfanin siminti a jihar Edo..

Tun a shekarar 2013 aka soma saninsa a sahun attajiran afirka. Amma dai, a shekarar 2014 jaridar attajirai ta Forbes ta lissafa shi a matsayin attajiri na 33 a Afirka da kadarorinsa na kimanin dala biliyan daya da rabi.

Daga baya kuma, a shekarar 2015, forbes din ta shaida cewar Shine attajiri na biyar a fadin Najeriya.

Attajirin yana da aure, da ‘ya’ya, sannan yana bada tallafi wajen taimako kamar yadda tsarin ‘philantropism’ ya nuna.

Ya gina gagarumin dakin kula da yara na gaggawa a asbitin Malam Aminu kano wanda aka sanya sunansa, sannan kuma ya gina cibiyar Ilimin addinin musulunci a Jamiar Bayero dake kano.

Madogara:-
Forbes 2014
Forbes 2015
Taskar Hikayoyi, Sadik Tukur Gwarzo RN.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button