Kannywood

Jerin matan Hausa Fim Guda 10 da Suka fi Daukar Albashi mai Tsoka a masana’antar Kannywood

Masana’antar Kannywood Allah ya albarkaceta da kyawawan mata kimanin guda dari biyar na yankin nahiyar arewa, wadanda suke da kwazo, ilimi da kuma sura ta jiki

– Wannan ne yasa muka gabatar da wani bincike domin gano muku ainahin nawa ne jaruman suke samu a wannan masana’anta

– Hakan yasa muka zo muku da sunayen jarumai mata guda goma wadanda suka fi daukar albashi mai tsoka a masana’antar daga shekarar 2018 zuwa 2019

A wannan karon mai makon mu fara daga ta daya, zamu dauko daga sama ne, ma’ana daga kan ta goma zuwa ta daya.

10. Zainab Indomie (N725,000)

Zainab Indomie ta zamo ta goma a cikin jerin sunayen bayan dawowar ta masana’antar a shekarar 2018.

9. Fati Washa (N905,000)

Fati Washa ta kasance kyakkyawa mai amana da hakuri, hakan ne ya bata damar zuwa ta tara a cikin jerin jaruman.

8. Maryam Booth (N1,267,000)

Maryam Booth wacce aka fi sani da Dijangala ita ce tayi sa’ar zuwa a matsayi ta takwas a cikin jaruman.

7. Maryam Yahaya (N1,449,000)

Ta bakwai a cikin jerin ita ce fitacciya kuma sabuwar ‘yar wasan nan  wacce tauraruwarta ke haskawa a wannan lokacin Maryam Yahaya.

6. Halima Atete (N1,811,000)

Fitacciyar jaruma Halima Atete ita ce ta yi nasarar zuwa ta shida a cikin jaruman.

5. Jamila Nagudu (N2,445,000)

Jamila Nagudu wacce kwanan nan ta dan yi sanyi a cikin harkar fina-finan ita ce ta zo ta biyar a cikin jerin ‘yan wasan.

4. Aisha Tsamiya (N2,535,000)

Aisha wacce aka fi sani da tsamiya ita ce ta samu nasarar zuwa ta biyar a jerin jaruman mata.

3. Hadiza Gabon (N2,952,000)

Hadiza Gabon wacce aka santa a bangaren taimakon gajiyayyu da marasa karfi ita ce ta yi nasarar zuwa ta uku a cikin jaruman.

2. Nafisa Abdullahi (N3,260,000)

Fitacciyar jarumar nan wacce tayi suna a fim din ‘Sai Watarana’ ita ce ta yi nasar zuwa ta biyu a cikin jerin matan.

1. Rahama Sadau (N3,622,000)

Fitacciyar jarumar nan ‘yar jihar Kaduna, wacce jama’a suka dinga yin cece-kuce akan halayenta ita ce ta zama zakaran gwajin dafi a cikin jerin jaruman.

Shafin Hausaloaded ta samu wannan labarin ne daga jaridar legit.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button