Duk Kasar Da Zatayi Wasa Da Nigeria Tana Tsoron Ahmad Musa, -Inji Yobo
Tsohon dan wasan baya na tawagar Super Eagles ta Najeriya kuma tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Eberton, Joseph Yobo, ya bayyana cewa duk kasar da zata hadu da Najeriya tana tsoron hatsarin Ahmad Musa.
Ahmad Musa, wanda ya buga dukkan wasannin da Super Eagles ta buga a gasar ta bana dai kawo yanzu kwallo daya kawai ya taimaka aka zura a raga sai dai duk da rashin zura kwallon a raga yana da tasiri sosai a tawagar ta Najeriya.
A wasan farko da Super Eagles ta buga da Burundi Ahmad Musa yazo a benci ne amma banda nan kuma kowanne wasa dashi ake farawa kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen ganin Super Eagles din ta cigaba da samun nasara.
Yace “Kowanne lokaci Najeriya tana samun fitattun ‘yan wasa wadanda suke fitar da kasar kunya kuma idan ana maganar ‘yan wasan gaba wadanda suke hargitsa kowacce irin baya tabbas a yanzu akwai su a Super Eagles” in ji Yobo
Ya cigaba da cewa “Kawo yanzu dai babu kamar Musa a cikin tawagarmu saboda yadda yake buga kwallo kuma yake wahalar da ‘yan baya da gudun da yakeyi da kowanne dan baya ya samu sannan ni kaina yanzu idan ka tambayeni dan wasan da bana son haduwa dashi a wanann gasar zance maka Ahmad Musa’
Yobo ya kara da cewa duk lokacin da Musa ya dauki kwallo zakaga abokan hamayyar Najeriya suna komawa baya suna tsorata saboda tasirinsa kuma idan kana da dan wasa kamar Musa tabbas zaka dinga samun nasara
A karshe kuma yace idan har Super Eagles tana son samun nasara akan Algeriya dole sai sun buga wasa sama da wanda suka buga a wasan Africa ta Kudu saboda kana yin nisa gasar tana sake yin wahala.