Kannywood

Darasin Cikin Fim Din ‘Wakili’ Sabon Salo Ne – Falalu Dorayi

Advertisment
Ga duk mai kallon fina-finan Hausa na lokutan baya zai ga kusan duk sakon daya ne, babu wani sabon abu da ke ciki, shi ya sanya mutane dama masu bibiyar masana’atar samar da fina-finai, za ka ga da zarar mutum ya fara kallon fim zai iya cewa abu kaza ne zai faru a kusan karshen fim din, saboda wannan matsalar gami da rashin samar wa da masu kallo abin da suke da bukata ya sanya wasu ma suka daina bibiyar kannywood din ma gaba daya.
To! Amma yanzu an fara samun gyara sosai don duk fim din da za’a kaishi ga sinima a gaskiya ba karamin aiki ya samu ba, saboda su sinima suna da nasu ka’idojin da suke dubawa kamin su amince su fara haska fim, wannan fa sanya yanzu dole duk wanda yake da bukatar nuna fim a sinima dole sai ya cika ka’idojin da ake bukata daidai da manyan sinima na duniya.
Kamfanin shirya fina-finai guda biyu ne suka bata tsawon lokaci domin samarwa da masu kallo sabon fim dinsu mai suna Wakili, wannan fim din shiri ne na tsagwaron ban dariya sakamakon soyayya.

‘Garkuwa empire da dorayi fims’ sune suka fito da fim din wakili.Labarin wakili wani mai sarautane wato Bosho, wanda ya kasance shugaba ne na gundumar da yake mulka amma kuma ya dauki wani salo mai makon adalci, sai rashin adalci. Shi dai Bosho duk wani hali na rashin gaskiya ya hada a cikin fim din.

Sannan gashi baya jin kunyar kowa ko ganin girman kowa a cikin fim din. Sannan yakan siyar da kayan mutane kama daga filaye babu abunda ya dame shi akan mai zai je ya dawo, amma fa a cikin sabon shirin wakili.
Wani abun mamaki kuma a game da shirin wakili shi ne duk wata fitowa a cikin fim din zai s aka dariya.

Da yake karin haske a game da fim din wanda ya ba da umarnin shirin Falalu Dorayi, ya ce, “A gaskiya nakan dade ban yi fim ba sakamakon wasu matsalolin, za ka ga mutum ya zuba amma ba za ka samu ribaba in ma an ci sa’a kamayar da kudaden ka”.

Da aka tambaye shi a game da nuna fim a sinima sai ya bayar da amsar cewa, “ni da ba na shawa’ar kai fim sinima saboda ba zuwa ake sinima kallo ba amma yanzu Alhamdulillah ana zuwa sinima sosai kuwa don ana kallo sosai.”
Ya kara da cewar “ina tabbatar wa masu kallon fim din wakili za su sha mamaki saboda sabon salo na ban dariya, duk wanda ya fito a cikin shirin wakili kawai bandariya yake bayarwa.”
Fim din wakili ya samu ingantaccen aiki tun daga samar da labari daukar shirin duk an yi shi a kan ka’ida.Jariman da suka baje basirar da Allah ya basu sun hada da Ali Nuhu, Suleman Bosho, Falalu Dorayi, Naburaska, Garzali Miko, Hadiza Gabon, Aisha Tsamiya da sauransu.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button