Dalilan Da Ke Haddasa Gushewar Imani Da Tausayi A Zuciyar Mata
Daga Garba Tela Hadejia
An shiga ruɗani kan yadda aka samu labarin wasu mata sun daɓawa wasu mazaje makami a Jihar Kano. Ɗaya ta daɓawa mijinta, ɗaya kuma ta daɓawa yayanta. Duk da cewar ba wannan ne karon farko ba a Nageriya. Akwai misalai da dama na yadda Mata su ka kashe mazajensu ta hanyar daɓa musu makami da kuma zuba musu guba a abinci.
Amma wannan lamari na baya-bayan nan, ya zo wa da kowa mamaki, kuma har ya zuwa yanzu jama’a na cigaba da tafka muhawara akai.
Sanin kowa ne Allah dai ya halicci mace kan rauni da kuma gajeren tunani. Akwai mamaki matuƙa ace mace ta iya ɗaga makami ta daɓawa wani. Duba da irin ɗumbin tausayin da Allah ya yi wa halittar ƴa mace fiye da ta ɗa namiji.
Ba wai nufin rubutuna ba wa mata masu irin wannan hali kariya ko uzuri ko lasisin cigaba da illata maza ko duk wata halitta ba ne. A’a zan dai yi ɗan tsokaci ne gwargwadon hali kan dalilan da ya sanya zuciyar wasu matan ke bushewa ta ƙeƙashe su aikata duk abin da zuciyarsu ta raya musu. Bisa hasashe da nazari da ƴar fahimta irin tawa.
Auren Dole: matsala ko dalili na farko da ke ƙeƙasar da zuciyar mace imani ya fita a ruhinta shi ne tilasta mata Auren wanda ba ta so. Domin baƙin cikin ta auri wanda ba ta so zai iya hassalata ta yadda da zarar sun samu wani ɗan saɓani ko ya yi mata ba daidai ba, to za ta iya kashe shi, domin dama ya isheta ƙyas ta ke jira su rabu. Ƙaramin tunaninta ba zai ba ta damar hakaito irin cakwakiyar da za ta faɗa a sanadiyar abin da ta aikata ba.
Kuma dama haka Allah ya halicci zuciyar ƴa mace kan Aure inde ta ce ta na so to ta na so ɗin. In ko ta ce ba ta so, to zaman lafiya ɗaya kawai a haƙura da wannan aure.
Ko da a zamanin iyaye da kakanni fa matan haƙuri su ka yi su ka yi biyayya wa iyayensu su ka karɓi mazajen da ba sa so, har ma ka ga mace faram-faram har da ƴaƴa barkatai a gidan miji amma da za ka tsaga zuciyarta ka gani za ka ga mijin nan fa ta na zaune da shi ne kawai saboda bin umarnin iyaye.
Akwai mutumin da aka ce irin haka ta taɓa faruwa da shi. Wato ya jima da matarsa har sun haifi ƴaƴa sun kuma samu jikoki barkatai. Wata rana su na zaune su na taɗi irin na mata da miji, sai ya ce mata “ikon Allah! Wance da fa ba kya so na da ƙyar ki ka yarda aka yi wannan aure”. Buɗar bakinta sai ta ce da shi “au wai a zatonka yanzun sonka na ke ? Ai kawai cika umarnin iyaye da biyayyar aure ne su ka sanya na ke zaune da kai”. An ce fa har jikoki ne da su. To wannan ita ake kira da mace, in ba ta so to fa ba ta so.
Yanzu kuma zamani ya sauya ƴaƴan yanzu ba sa yarda da wannan. Ba kowacce mace ce za ta yarda ayi mata auren dole kuma a zauna lafiya ba.
Ta’ammali Da Kayan Maye:- wannan ita ce matsala ta biyu ko dalili na biyu, mata da dama yau sun faɗa cikin harƙallar shan miyagun ƙwayoyi, wato kenan ƙaramar ƙwaƙwalwa ta haɗu da kayan maye ta sha ta bugu, duk yadda ka baƙanta mata, to za ta iya aikata komai akan ka domin ganin ta ɗauki fansa.
Rashin Kulawa Da Ƙuntatawa Da Takurawa:- a duk lokacin da ka takurawa mace, ba ma mace kawai ba, duk wata halitta me rauni da za ka takurawa ka kuntata mata ka matsa mata, alhali ma kuma dama babu wata kulawa ta rayuwa da ka ke ba ta, to fa wannan matsi zai ya sanya wa zuciyarta ta bushe ta ƙeƙashe ta ji ba ta shakka da tsoron komai.
Wato ma’ana kalmar nan ta Bahaushe da ya ke cewa “tura ta kai bango”. Ta na tasiri cikin zuciyar wasu matan. Ai ko wacce ake tuhuma da kashe ƴaƴanta a Jihar Kano, kwamishinan ƴan sanda na Jihar ya shaidawa sashen Hausa na (BBC) cewar a binciken da su ka gudanar, dama can akwai ƴar tsama tsakaninta da yayan nata, kuma wannan ta sake faruwa a tsakaninsu har ta kai ta ga aikata masa ba daidai ba.
Kenan ƙila da ma can ya shiga rayuwarta ya tukura mata kuma ba ya iya yi mata komai na kyautatawa irin na tsakanin wa da ƙanwa.
Allah ya ji ƙan marigayi Shaik Ja’afar Mahmud Adam, a wani lokaci Malam ya ce: “ko dabba ka takurawa, muzuru ko mage har ka kai shi bango to fa in ya rasa hanya zai iyo baya ne ya biyo ta kanka, sai dai duk abin da zai faru ya faru”.
Wato abin da na ke son mu gane akan wannan gaɓa shi ne: yaya ne kai ko Miji ga mace, kar ka zamto mai kaurin hali da takura mata kan komai a kowane lokaci.
Ka ƙaunaceta ka nuna mata soyayya ka ba ta kulawa ka kyautata mata, haka mace ta ke so ta ga ka maishe ta tamkar wata ƙaramar yarinya ƴar cira wajen tattali da kulawa.
Muddin ka yi mata haka to ai wani abun ba ma sai ka ce ta bari ba, ko da kowa zai hanata yin wani abu na ba daidai ba ta ƙi hanuwa, to kai ganin fuskarka agun kaɗai ko ba ka ce ta bari ba, ya isa ya sanya ta fasa.
Duk halittar da za ka ja a jika ka kyautata mata ko da kuwa akwai wancan dalili na farko wato (ƙiyayya), muddin babu wancan dalili na biyu wato (gushewar hankali ta sanadiyar shan kayan maye), to ba wai kallon ta ɗauki makami ta daɓa maka ba, ko da wani ta gani zai illata ka, to sai fa inda ƙarfinta ya ƙare wajen ba ka kariya.
Faɗa ce ta manzon Allah (S.A.W) duk zuciya ta na ƙin duk mai munana mata, ta na kuma ƙaunar duk mai kyautata mata. Mun yi imani mun gaskata duk abin da manzon Allah (S.A.W) ya faɗa haka ya ke.
A dunkule: mun fahimci cewa auren dole da shan miyagun ƙwayoyi da rashin kulawa da takurawa da kuntatawa da matsi, duk dalilai ne da ke sanyawa tausayi ya kau a zuciyar mace har ma ta bushe ta ƙeƙashe ta aikata duk abin da ranta ya raya mata ta yadda kuma gajeren tunani da Allah ya yi musu ya hana su gano matsalar da za su iya faɗawa a sanadiyar aikata ba daidai ba.
-Garba Tela Hadejia
Litinin, 8/7/2019.