BOKO HARAM : Buhari Ya Nuna Takaicin Sa Game Da Kisan Mutum 63 a Maiduguri
An tabbatar da cewa Boko Haram sun kashe jama’a masu yawa a wani hari da suka kai, inda su ka bude wa masu zaman makoki wuta a Maiduguri.
An ce sun kai harin ne jiya Lahadi wanda Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da kisan jama’a da yawa.
Wasu kafafen yada labarai sun ce mutane 65 aka kashe a wurin makokin.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar da dare, ya ce Buhari ya yi Allah-wadai da wannan kisan gilla da aka yi wa mutane masu yawa.
Shugaban Kasa ya samu tabbaci daga hukumomin tsaro na sojoji cewa, “yan ta’addar da suka aikata wannan mummunan kisan kiyashi za su dandana kudar su.” Haka Shehu ya bayyyana a cikin takardar manema labarai da ya fitar jiya Lahadi.
“Gwamnatin Tarayya na daukar kwararan matakai da suka wajaba domin kare kasar nan daga hare-hare. Wannan gwamnati na kokarin ganin ta kakkabe masu ta’addanci.” Inji Buhari ta bakin Garba Shehu.
Daga nan ya kara da cewa an fara shirye-shirye farauto wadanda suka yi wannan kisa ko ma a ina suka boye. Tare da cewa sojojin sama da na kasa na can na farutar su.
Buhari ya kara tabbatar wa mazauna Maiduguri da ukkan ‘yan kasar nan cewa za a tsaurara matakan tsaro a Maiduguri da sauran sansanonin masu gudun hijira.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga Dokin karfe Tv a facebook, Wannan mummunan kisa da Boko Haram suka yi a Maiduguri, ya zo daidai makon da aka cika shekaru 10 cur ana fama da hare-haren Boko Haram.
Gwamnatin Buhari ta sha cewa ta kakkabe Boko Haram. Haka ma Babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai, ya sha furta wannan ikirari.
Sai dai kuma a kullum Boko Haram sai hari suke kara kaiwa.
Idan za a iya tunawa, tsohon gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam kasa zuwa garin su ya yi domin ya jefa kuri’a a zaben 2019 da ya gabata, saboda hare-haren Boko Haram.