Tirkashi: Ran jaruma Saratu Abubakar ya baci tayi kaca-kaca da masu kudi da suke daukar ‘yan mata suna lalata da su
Jarumar ta yi Allah wadai da manyan masu kudi da suke bai wa ‘yan mata kudi suna yin lalata dasu
– Ta ce bai kamata suje su dinga kulle ‘ya’yansu a gida ba suna zuwa suna daukar ‘ya’yan talakawa suna batawa ba
– Ta shawarci ‘yan mata akan su daina amincewa da tsofaffin masu kudi, domin duk wacce suka bata karshenta ba zai yi kyau ba
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da take tasowa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood , Saratu Abubakar ta yi kaca-kaca da manyan masu kudi masu daukar ‘yan mata suna basu kudi su yi lalata dasu.
A wani bidiyo da jarumar ta dauka mai tsawon minti daya, wanda ta aikawa kafar yada labarai ta Aminiya, ta yi Allah wadai da dabi’ar manyan masu kudin da suke yin lalata da ‘yan mata ba tare da tunanin abin da zai je ya dawo ba.
Ta bayyana cewa irin wadannan masu kudin zaka tarar sun boye nasu ‘ya’yan a gida sun basu tsaro sosai a cikin gida, inda koda fita zasu yi sai an hada su da wani ya lura dasu, amma sai su dinga zagayewa suna zuwa suna daukar ‘ya’yan talakawa suna basu kudi suna kwanciya dasu.
Ta ce: “Yarinya karama ‘yar shekara 17 zaka je ka dauka kayi lalata da ita, amma kuma kai kaje ka kunshe naka a cikin gida, idan zasu fita sai ka sa wani ya kula dasu, babu damar su fita suji dadin rayuwarsu, kai kuma zaka je ka dauki dubu hamsin ka bai wa yarinya kayi lalata da ita, wa kake yiwa wayo?”
Ta kara da cewa: “Yanzu idan ka dauki naira dubu hamsin ko dari ka baiwa wannan yarinyar da kake so kayi lalata da ita, kace taje ta kama sana’a, ba tare da kayi lalata da ita ba, kasan irin yawan ladan da zaka samu saboda wannan kawai?
“Amma ina, sai dai kayi ta kwanciya da ita, wasu ma har cewa suke su basu son manyan mata, sai yara kanana ‘yan shekaru 17 zuwa 18. Saboda tsabar rashin tsohon Allah,” in ji jarumar.
Saratu ta bai wa ‘yan mata shawara akan su daina yarda da manyan masu kudi, domin duk wacce suka batawa rayuwa nan gaba sai ta yi dana sani.